27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Wani mutumi mai sana’ar sayar da motoci ya kurma ihu bayan ganin tsadadiyar motar Lamborghini da mawaki Davido ya siya

LabaraiWani mutumi mai sana'ar sayar da motoci ya kurma ihu bayan ganin tsadadiyar motar Lamborghini da mawaki Davido ya siya
bfb7e7a55a7b56aa
wani mutumi mai sana’ar sayar da motoci ya kurma ihu bayan ganin mawaki Davido a motar lamborghini da ya siya

Wani dan Najeriya a shafinsa na Twitter mai suna @nugway ya janyo cece-ku-ce a duniyar yanar gizo bayan ya yada wani hoton bidiyo a shafinsa. Mutumin wanda ya kasance, dillalin motoci ne ya sami sa’a yayin da ya yi nasarar yin ido biyu da motar zamani Lamborghini a karon farko.

Motar mai tsada ce sai wane da wane

Abin birgewan shine motar mai tsada ce da ba kowani mahaluki ya mallake ta ba sai manyan yara irin su, Davido.
Cikin farin ciki da zumudi mutumin Bai tsaya bata lokaci ba ya yi charaf ya fada shafin sa na Twitter inda ya sanar da duniya cewa ya ga mawaki Davido a cikin motar Lamborghini a unguwar Ikoyi a Legas.

Kadan daga cikin martanin Masu amfani da shafukan sada zumunta

H ya rubuta: “Dubi yadda hantar cikin ka ke tsalle.”

@Snakeystunna ya ce: “ganin Davido ne ya saka ihu ko lambo? Wanne a ciki”

@insaynworld ya rubuta: “Omo dubi yadda yake farin ciki inda kasar Amurka ne da kaji karar harbi.

@ydfk_amaka ya ce: “Yaya kuke tsammanin jikin sa ba zai yi kyarma ba? Ya yi ido biyu da 001??? Wo! Ai ko ni ne jikina bari zai yi.”

Yan kudu sun hau fargaba akan ko dai Genevieve ta musulunta bayan ta yi wallafa da ayar Qur’ani, dadduma da kabari

Jarumar masana’antar fina-finan kudu, Genevieve Nnaji ta saki wani gajeren bidiyo a shafin ta na Instagram ya tayar da kura inda aka dinga musayar ra’ayi dangane da bidiyon, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gajeren bidiyon ya nuna tunatarwa ne akan cewa duniyar nan ba komai bace ba a harshen turanci.
A bidiyon an nuna cewa lahira ce tabbatacciya kuma komai na duniyar nan mafalki ne ba gaskiya ba.

Bidiyon ya nusar da mutane akan su farka, kuma an sanya ayar Al’Qur’ani mai girma da kuma dadduma.

Kamar yadda ake fadi a cikin bidiyon:

“Don Allah! Don Allah! Ku farka! Ku farka! Ku farka! Ko wanne mai rai mamaci ne.”

Bayan ta wallafa bidiyon nan, ya zama abin surutu da kuma fargaba, inda masoyanta musamman ‘yan kudu suka hau cece-kuce.
Sun yi fargaba akan kada fa ace jarumar nan ta musulunta ko kuma shirin musulunta take yi, idan ba haka ba, tana kirista, mai zai hada ta da wallafa ayar Qur’ani, dadduma ko kuma makabarta?

Duk da dai a bangaren story ta wallafa bidiyon kuma bayan awa daya story ke bata a Instagram. Amma sai wata ma’abociya instagram mai suna poshjournal ta kwafo kuma ta wallafa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa@gmail.co

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe