27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ku dage wurin neman kudi, nan gaba muna sa ran amshe fiye da haka a wurin ku, ‘Yan fashi ga fasinjojin da suka tare

LabaraiKu dage wurin neman kudi, nan gaba muna sa ran amshe fiye da haka a wurin ku, ‘Yan fashi ga fasinjojin da suka tare

‘Yan fashi da makamin da suka tare fasinjojin da ke tafiya Kumasi, Ghana, sun shedawa wadanda suka tare da su je su nemi kudi, saboda zasu sake tare su nan ba da jimawa ba, LIB ta ruwaito.

An tattaro yadda tawagar ta kunshi ‘yan fashi 7 ta kai hari ga wasu direbobi da fasinjoji da misalin karfe 1:00 na daren Litinin, 21 ga watan Maris, a Assin Endwa cikin arewancin tsakiyar yankin.

yan fashi
Ku dage wurin neman kudi, nan gaba muna sa ran amshe fiye da haka a wurin ku, ‘Yan fashi ga fasinjojin da suka tare

Kamar yadda kananun jaridu suka labarta, barayin da suka rufe fuskokin su, basu tsaya a kwace mahimman abubuwa daga mutanen da suka tare ba, sai da suka nada wa wasu fasinjojin duka.

Wasu daga cikin wadanda lamarin ya auku da su, yayin bayyana kalubalen da suka fuskanta, sun bada labarin yadda ‘yan fashin suka ce musu suje su kara dagewa wajen neman na kansu, yadda zasu ci gaba da samun damar amshewa daga wurin su a wani harin da zasu kai.

An kwace wa fasinjojin wayoyinsu, jakunkunan tafiyar su da kudadensu. ‘Yan fashin sun kara da tafiya da mukullen manyan motoci uku da wata motar kaya dauke da abubuwa.

DSP Moses Osakonor, kwamandan ‘yan sandan Assin Praso, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce, tawagar barayin ta tare titin inda ta dakatar da wata motar kaya sannan ta aiwatar da fashin.

Osakonor ya ce, ‘yan sanda sun shirya dakile harin ‘yan ta’addan.

Haka zalika, an tattaro bayanai akan yadda barayin suka kai wa kungiyar kwallon kafa ta Ashantigold farmaki a wuri daya, cikin dare bayan buga wasa tsakanin GPL da Hearts of Oak.

“’Yan ta’adda sun kai mana hari akan hanyar dawowarmu daga Accra a Assin Edwa. Inda barayin suka harba harsasai uku a gaban gilashin motar mu mara jin harbi a lokacin da direban kungiyar ya kutsa cikin taron masu harbe-harben. Cikin sa’a, babu wanda ya samu wani rauni. Gaba daya kungiyar tana cikin koshin lafiya a Obuasi,” A cewar kungiyar ta wata takarda.

Sai dai, ana shawartar mutane masu tafiyar dare da su zama masu kula, sannan su yi hakanne idan ya zama dole.

Kano: Budurwa ta aika wa saurayinta ‘yan fashi saboda yace ya daina son ta

Wata kotun majistire mai lamba 18 dake zaune a unguwar Gyadi-Gyadi dake jihar Kano, tayi watsi da bukatar bada belin wata budurwa da take zargi da aika wa saurayinta gungun ‘yan fashi.

A zaman shari’ar da aka yi a kotun ranar Alhamis, Alkalin kotun Mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman, ya ki amincewa da bukatar da lauyoyinta suka nema, inda suka bukaci a basu belinta da kuma matasan da ta tura su afkawa saurayin nata.

Kamar yadda jaridar gidan Radiyon Freedom dake jihar Kano ta ruwaito, a ‘yan kwanakin da suka gabata ne dai ake zargin wannan budurwa mai suna Fatima Umar, wacce ke zaune a yankin Dantsinke da ke cikin karamar hukumar Kumbotso, da aika wa saurayin nata wasu gungun matasa har guda 6 dauke da muggan makamai, har cikin gida, akan kawai yace ya daina son ta.

A karshe dai Alkalin kotun, Mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ya dage sauraron wannan kara har zuwa ranar 30 ga wannan wata na Disamba da muke ciki, inda za a cigaba da sauraron karar budurwar da saurayin.

Mutumin dai an ruwaito cewa ya kware matuka wajen damfarar mata, inda yake da halayya ta aurar mace, sai ya dinga gallaza mata, hakan zai tilasta ta nemi a raba aurensu, a karshe kuma kotu za ta bukaci dole sai ta mayarwa da mutumin sadakinsa.

A karshe dai asirinsa ya tonu, bayan matarsa ta karshe ta rubutawa kotu dukkan irin abubuwan da yake yi mata, kotun ta bayyana cewa matar baza ta biya shi ko sisi ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe