27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Miji,mata da ‘yayansu sun tsallake rijiya da baya,yayinda fankar sama ta rufto musu

LabaraiMiji,mata da 'yayansu sun tsallake rijiya da baya,yayinda fankar sama ta rufto musu
642542ca6592c68f
miji,mata da yaransu sun tsallake rijiya da baya yayin da fankar sama ta rufto musu a kai

Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Yvonne Stanley ta ba da labarin yadda ita da iyalanta suka tsallake rijiya da baya. A wani sakon da ta wallafa a Facebook a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, ta bayyana cewa fankar su ta fado kan gado a daidai lokacin da ita da mijinta su ke shirin kwanciya.

Yvonne ta kasa daina mamakin yadda wannan lamari ya faru ta kara godewa Ubangiji da ya ceto rayuwar su

Yvonne ta kasa daina mamakin wannan al’amari cikin ikon Allah fankan ta rufto ba tare da taba yaran ta da ke kwance a kan gado ba duk da ‘ yadda su ka baje suna kwasar baccin su.’
Ta kara da cewa fankan ya fado ne a dai dai wurin da suka saba zama ita da maigidanta,abin da ya,hana fankar fadowa kansu ba su zauna a wurin ba ne a wannan lokacin. Abinda ta ce kamar haka:

Ba zan iya yin shuru ba game da wannan lamari ba ooooo… Da yanzu ‘yaya na sun zama marigaya,da rudewan yafi haka.
Ina jin labarin yadda ake samun asaran rayuka a hadarin fanka, babu wanda ya yi tsammanin haka.

A daren jiya da misalin karfe 11:15 na dare, a gaban idan mu ni da mijina fankar sama tana tsaka da aiki ta rufto kasa ba tare da wani sauti ko alama ba.
“Yadda Allah ya tsare wadanna yaran ya tura su gefe guda duk da “yadda suke bajewa in suna bacci”. Ya kara tsaremu ni da mijina ba mu zauna wurin da muka saba zama ba. Allah ya kaddara kaifin fankar nan ba zai cutar da mu ba.
“Dubi irin yadda su ke juyi dai dai lokacin da na dauki wannan hoton. Mai kake ganin zai faru in da fankar ta fado a kansu. Da kafar su zata gutsire “me Idan
“…”

Yan Najeriya sun taya Yvonne godewa Allah

Patience Etim ta ce: “Allah abin godia,mu’ujizar Sa mara iyaka.”

Anietie Idung ta ce: “Wannan shi ne karo na biyu da nake ganin haka. Na farko, abin ya faru ne a cocin da nake zuwa yayin da ake tsaka da bauta amma cikin ikon Allah, matar da abin ya sameta bata ji rauni sosai ba.”

Charlie Ifo ya ce: “Hakika Allah abin godiya, da abin ba zai yi dadin fadi ba. Na gode Yesu. Zai ci gaba da ba makiya kunya.”

Wani dalibin Yukirain dan Najeriya ya mutu a sakkwato, sati biyu kacal bayan an tseratar dasu
Wani dalibi dan Najeriya mai suna Uzaifa Halilu Modachi, da yake karatu a kasar Yukirain ya mutu, a garin Sokoto, sati biyu kacal bayan dawowar sa Najeriya.

Kafin rasuwar sa Halilu Modachin, ya zauna a kasar Yukirain din tsawon shekara uku ba tare da ya dawo hutu gida Najeriya ba.
Dan shekarar karshe a karatun sa, a jami’ar lafiya ta Zaporozhye, yana kan shirin fara jarrabawar karshe ne yaki ya barke tsakanin Yukirain din da kasar Rasha.
Da yake bayyana alhininsa, baban mamacin honarabul Habibu Haliru Modachi, dan majalisa a jihar Sokoto, yace :

” Alhandulillah, Allah shine ya bayar da rayuwa , kuma ya karbi abarsa, haka ya tsara abin sa kuma bamu da ja akan hakan”
Da ace a kasar Yukirain ya rasu, sai an fadi abubuwa da yawa akan sa, ko ace sojojin Rasha ne suka kashe shi, ko ace yayi hadari, ko kuma ace sojin Yukirain ne suka harbe shi.

” Muna matukar godiya ga Allah da ya sanya ya mutu a gabanmu, muna kuma matukar godiya ga gwamnati, musamman ta jihar Sokoto, saboda kokarin tseratar dasu da tayi tun kafin rincabewar yakin na Yukirain. “

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe