24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Jarumin maza: Yadda wani mutum ya yi takarar aure da dan Sarkin Aljanu a Kano

LabaraiJarumin maza: Yadda wani mutum ya yi takarar aure da dan Sarkin Aljanu a Kano

Ana zargin wani saurayin matashin aljani da yunkurin kwace wa wani mutum matarsa ta aure, sai dai Allah ya yi wa mutumin taimako, kasancewar sa mai yawan addu’o’i da kuma azkar.

Mutumin ya dage wurin yawaita karatun Al’Qur’ani da addu’o’i a gida da waje har ya samu dakyar matashin aljanin ya kyale masa matar sa.

dan sarkin jinnu
Jarumin maza: Yadda wani mutum ya yi takarar aure da dan Sarkin Aljanu a Kano

Bayan nan ne matashin aljanin ya sauya salo, inda ya fara yi wa mutumin tayin kudade masu tarin yawa kimanin Naira miliyan dari uku don ya taimaka ya bar masa matar.

Sun ci gaba da dauki ba dadi da aljanin kamar yadda mutumin ya shaida wa Dala FM:

“Ya ce min shi yana son ta ne tuntuni, in zo mu yi sulhu da shi. Kuma abinda ya sa na aureta saboda ina da yawan addu’o’i da azkar. Kuma shi yana sonta:

“Ya ce min shi dan sarkin aljanu ne. Yake ce min me zai ba ni in bar masa matata? Sai ya ce zai bani miliyan 100 in ina bukata, na ce a’a.

“Sai yace mu yi maslaha ni da shi, kar in zo wurin mai gida Kacaku. Sai yace zai ban miliyan 200 in na yarda. Sai nace mishi gaskiya ni ba irin wannan hanyar nake so ba. Ina dan almajirci na. Ina neman ‘yan hakkoki na wurin Allah.

“Sai yace min in na yarda zai bani miliyan 300, idan ina kokwanto ma yanzu in bude daki na, zan ga kudin. Sai nace mishi a’a.”

Ya ci gaba da shaida cewa shi lebura ne a kasuwa yake yin ‘yan ayyukan sa, don haka ba ya bukatar kudin hannun aljanin.

Ya shaida yadda aljanin ya bayyana masa cewa shi ne ya hana ta haihuwa tsawon shekaru 2 da suke zaune a matsayin mata da miji.

Mutumin ya ce sun ci gaba da dauki ba dadi da aljanin akan cewa tabbas yana mutukar son matar sa.

Wakilin Dala FM ya ce za su ci gaba da bibiyar lamarin don su ji yadda ta kaya.

Tirkashi: Har da Aljanu a masoyan jarumi Ali Nuhu

Jarumi Ali Nuhu ya samu masoya har cikin aljanu. An tura wani sako ta shafin Northern blog na Instagram mai ban mamaki.

Dama a kan yi wallafe-wallafe a shafin a kan lamurran rayuwa har da wayar da kan jama’a da wasu lamurra masu wata ban al’ajabi.

Wani ya wallafa yadda wata ‘yar uwarsa mai aljanu ta ke yawan kiran sunan jarumi Ali Nuhu idan sun tashi.

Kamar yadda sakon ya zo:

“Malam Khalifa ina wuni? Yau wani abu ne ya faru a gidanmu, wato masoyan Ali Nuhu ba a mutane kadai suka tsaya ba har da Aljanu.

“Wata yarinya ce a gidanmu take da aljanu su na yawan cewa ‘Sai Ali Nuhu’, da su ka tashi ta neman sai an kai ta wurin sarki Ali Nuhu, da kyar aka kamo ta.”

Ya kara da bayyana yadda idan ana so ta yi wani abu a gida sai an ce mata ‘Don sarki Ali Nuhu ko kuma FKD.

A cewarsa lallai Ali Nuhu ya cika jarumin duniya.

Take a nan jarumai su ka fara tsokaci iri-iri dangane da wallafar, har jaruma Aishatul Humaira da Lukman na Kwana Casa’in su ka ja hankalin Ali Nuhu a kan wannan wallafa.

Ali Nuhu ya kuwa amsa kiran da jaruman su ka yi masa inda ya zo bangaren tsokaci ya ce “Aljanu kuma? Cike da alamar mamaki.

Aishatul Humaira kuma ta amsa shi da cewa “haka aka ce.”

Take anan jama’a su ka dinga tsokaci a karkashin wallafar, yayin da abin ya ba wasu dariya wasu kuma suka nuna mamakin su karara.

Tabbas ba lallai hakan ya zama abin mamaki ba, don harkar sana’ar sa ta daukaka ce, zai iya burge mutum da aljan.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe