27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

‘Yan bindiga sun sako mutum 75 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara

Labarai'Yan bindiga sun sako mutum 75 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun sako mutum 75 waɗanda aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kekun Waje cikin ƙaramar hukumsr Bungudu ta jihar Zamfara. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mutanen da aka sako ɗin dai an ɗauke su a wasu manyan hare-hare da aka kawo a ƙauyen cikin watanni biyun da su ka gabata.

‘Yan bindigan da farko sun ɗauke mutum 61, sannan bayan kwanaki 36 sun sa ke kawo hari ƙauyen inda su ka ƙara ɗaukar wasu mutum 15.

Sun riƙe wata ƙaramar yarinya a wurin su

Sai dai ‘yan bindigan sun riƙe wata ƙaramar yarinya mai shekaru 6 mai suna Ummi inda su ka sanar da iyayen ta cewa sun amshi rainonta ne saboda ta na birge su.

Iyayen yarinyar ba su daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ɗaya daga cikin su ya ce bai taɓa haihuwa ba a rayuwar sa saboda haka zai yi rainon yarinyar.

Ta zama ɗiyar sa inda yayi alƙawarin zai ba ta kulawa mai kyau. Har yanzu yarinyar na wajen su.

Mazauna ƙauyen sai da su ka biya naira miliyan 4 kafin a sako su.

Waɗanda aka sako ɗin tuni har sun koma wajen iyalan su. Daga cikin sharuɗan da ‘yan bindigar su ka bayar akwai cewa dole ‘yan sakai su aje makaman su. A cewar wani mazaunin ƙauyen mai suna Sadiq

Ba a samu jin ta bakin hukuma ba

Ba a samu jin ta bakin kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton.

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da yawan gaske yayin da suke tsaka da shagalin bikin shugabansu a Katsina

Yan bindiga da dama sun rasa rayukan su yayin da sojojin sama, NAF suka dinga ragargazar su yayin da suke bikin daya daga cikin shugabannin su a Jihar Katsina, Jaridar Leadership ta ruwaito.

Cikin wadanda aka halaka har da Sule, wani shu’umin dan bindiga, wanda dan uwan Lalbi Ginsha ne, shi ma gagarumin dan ta’adda ne.

Kamar yadda PRNigeria ta ruwaito, lamarin ya auku ne a kauyen Unguwar Adam da ke karamar hukumar Dan Musa a Jihar Katsina.

Majiyar sirri ta bayyana yadda sojojin saman suka samu bayanan sirri akan cewa ‘yan bindiga sun bar Dan Alikima zuwa Unguwar Adam don shagalin bikin wani shugaban su

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe