22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Mutumin da aka bayyana ya mutu a masallacin Annabi Muhammadu SAW, yayin sallah ya farko 

LabaraiMutumin da aka bayyana ya mutu a masallacin Annabi Muhammadu SAW, yayin sallah ya farko 

Kwanannan aka karade yanar gizo da hotunan  wani mutum wanda aka ce yana tsaka da yin sun jaddar sallar Jumuah ya mutu, a masallacin Annabi Muhammadu SAW dake garin Madina, a ranar 18 ga watan Maris. 


Hoton ya nuna wani mutum ne a kwance magashiyan, a yanayin sujjada, inda mutane da yawa suka zagaye shi suna jimami da alajabi, gamida yi masa murnar dacewa a karshen rayuwar sa. 


Sujjada dai wani babban rukuni ne a cikin sallah a addinin musulunci , wanda yake nuna kaskantar da kai ga Allah a yayin da mutum yake fuskantar Alqibla. 

mutu
Mutumin da aka bayyana ya mutu a masallacin Annabi Muhammadu SAW, yayin sallah ya farko 


Kafar tweeter da ta yada labarin, sun nuna kyawun faruwar abin, ace karshen rayuwar mutum ya riskeshi yana cikin yanayin sujjada a sallar Jumuah, kafin daga baya su canja sakon da suka sanya tun farko. 

Yadda aka gane mutumin bai mutuba

Wasu mutane ne suka ankarar da jami’an tsaro bayan an sami mutumin magashiyan, inda akayi sauri aka garzaya dashi asibiti a cikin motar ambulas ta majinyata. 


Bayan yan gwaje-gwaje, sai aka gano cewa ba mutuwa yayi ba kawai dogon suma ne yayi lokacin da ake gudanar da sallar Jumuah din. 


A fadar mai magana da yawun, hukumar (red crescent ) ta Madina, yace jami’an agajin gaggawa na masallacin Madina sun tabbatarda cewa mutumin bai mutu ba, kuma yana samun kulawa a wani karmin asibitin yanki. 


Duk da dai har yanzu babu wani takamaiman labari akan mutumin, amma dai mutane na cewa shi dan asalin kasar Pakistantan ne. 


Lamari irin wannan yana faruwa a masallacin Madina, kwanaki ma an sami mutuwar wasu mutane biyu ana tsaka da sallah, daya a shekarar 2010 dayan kuma 2013.


Ana ganin mutuwa yayin sujjada, kuma a sallar Jumuah, musamman na a masallacin Annabi Muhammadu SAW, babban dace ne ga mutum na kyakkyawan karshe.

An amince da yin buda baki a masallacin Harami da na Annabi(SAW) bayan shekaru 2 da dakatarwa

A yayin shirye-shiryen maraba da watan Ramadan, shugaban hukumar kula da masallatan harami guda biyu ya sanar da cewa an bayar da izinin gudanar da liyafar buɗa baki a masallacin Harami bayan dakatarwar da aka yi na tsawon shekaru biyu sakamakon annobar COVID-19, theislamicinformation.com ta ruwaito.

An kuma sabunta izini ga masu samar da abinci mai saurin gaske a wuri mai tsarkin.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma sanar da cewa an bayar da izinin dawo da buɗa baki a masallacin Annabi da ke Madina.

Ana sa ran masallatan Harami guda biyu za su tarbi ɗimbin masu ibada a lokacin Umrah a Masallacin Harami da ziyartar masallacin Annabi a cikin watan Ramadan, wanda za a fara a farkon watan gobe.

KU KARANTA : Hukumomin Saudiyya sun ƙwace jabun ruwan zam-zam kimanin katan ɗari huɗu a Makkah

Hukumomin Saudiyya sun sassauta dokokin gudanar da aikin Umrah a baya-bayan nan bayan wani mataki da masarautar ta dauka, wanda kuma ya sassauta takunkumin hana yaɗuwar cutar COVID-19.

Wasu daga cikin matakan kariya da aka soke sun haɗa da soke izinin yin Sallah a Masallacin Harami da kuma soke gwajin riga-kafi ga dukkan mahajjata masu shiga Masallacin Harami guda biyu.

Bugu da kari, ma’aikatar Hajji da Umrah ta kuma soke rajistar bayanan riga-kafin ga al’ummar Musulmi a ƙasashen waje domin samun izinin Umra wanda a baya ya zama dole.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

https://youtube.com/watch?v=HbCdlCh0R74%3Ffeature%3Doembed

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe