24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Gidajen cin abinci ba za su sayar da abinci ba a lokacin azumin watan Ramadana, In ji hukumar Saudiyya

LabaraiGidajen cin abinci ba za su sayar da abinci ba a lokacin azumin watan Ramadana, In ji hukumar Saudiyya

Hukumomin Saudiyya har yanzu sun hana gidajen abinci sayar da abinci a lokacin azumin watan Ramadan.

Wata wasiƙa da aka yaɗa a yanar gizo kwanan nan ta haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta. Ta yi iƙirarin cewa za a bar gidajen abinci a Saudi Arabiya su yi abinci a lokacin azumin Ramadan na wannan shekara. A cewar wasikar, gidajen cin abinci za su iya ci gaba da sayar da abinci ga baƙi ko masu yawon bude ido muddin sun sanya labule ko kuma rufewa.

Saudi Restaurant
Gidajen cin abinci ba za su sayar da abinci bA a lokacin azumin watan Ramadana, in ji hukumar Saudiyya

Mahukuntan Saudiyya cikin gaggawa sun ɗauki kwararan matakai na mayar da martani ga wasikar don gujewa yaɗuwar ruɗani. Majalisar dokokin Saudiyya ta ce wasiƙar ta yi iƙirarin ƙarya har ma ta kira ta da ‘wasiƙar ƙarya.’

Saudiyya ta musanta cewa za a ba da izinin bude gidajen abinci da ba wa baƙi ko masu yawon buɗe ido abinci a lokacin azumin watan Ramadan.

A ranar Laraba, Majalisar ta yi kira ga jama’a da kada su yarda da labaran ƙarya da ke yawo a yanar gizo cikin sauki. Majalisar ta ce za a buga duk wani hukunci ne kawai a shafinta na intanet da kuma shafukan sada zumunta.

Ana ba da izinin ga gidajen cin abinci a cikin Masarautar da su yi aiki sa’o’i kaɗan kafin lokacin buɗa baki don ba da abinci.

A bara, hukumomi har sun sanya sabbin ƙa’idoji don hanyoyin tattara kayan abinci da ba da oda ta hanyar kafa tsarin isar da kaya a zaman wani bangare na matakan hana yaɗuwar cutar ta coronavirus.

Ramadan ya zo ne a kan wata na tara na kalandar Musulunci, wanda aka yi imanin cewa yana daya daga cikin mafi tsarki a watannin musulunci wanda shi ne Annabi Muhammad ya samu aka masa da kur’ani mai girma a cikinsa. A cikin watan Ramadan, Musulmai na duniya na yin azumi daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana a kowace rana na tsawon watan.

A watan Ramadan da ya gabata, Dubai ta ba da damar gidajen cin abinci su yi hidima ga abokan cinikayyarsu a lokacin azumin watan Ramadan ba tare da tantance su daga jama’a ba. A shekarun baya, gidajen cin abinci sun ba da izinin ba da abinci a lokutan azumi saboda ana buƙatar su yi aiki ga abokan cinikinsu yayin cin abinci a idon jama’a.

Za a dawo da shan ruwa a Masallacin Annabi cikin watan Ramadana bayan shafe shekara 2 da dainawa saboda COVID

A yayin da watan Ramadana mai albarka ke cigaba da karatowa, hukumar kula da harkokin Masallacin Annabi dake Madinah, ta bayyana kudurinta na dawo da shan ruwa a cikin Masallacin bayan shafe shekara biyu ba a yi ba sakamakon annobar COVID-19.

Don ganin an kare lafiya da rayukan al’umma, hukumar ta dakatar da shan ruwa a Masallacin na Annabi tun a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2020, wanda ya yi daidai da shekarar 1441 ta Musulunci.

Hukumar lura da harkokin Masallacin za ta dawo da shan ruwa a cikin Masallacin cikin watan Ramadana dake karatowa.

Sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa iya wadanda aka bawa lasisin yin hakan ne kawai za su samu damar shiga domin su gabatar da ibada da kuma buda baki.

Source: The Islamic Information

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe