24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Majalisar walikai ta Bukaci Bankuna da su dawo amfani da silalla da kwabbai

LabaraiMajalisar walikai ta Bukaci Bankuna da su dawo amfani da silalla da kwabbai
adae85eda6efd183
Majalisar wakilai ta bukaci Bankuna da su dawo amfani da silalla

An bukaci bankuna da su dawo biyan silalla

Abin mamaki, a ranar Talata, 22 ga watan Maris,shekarar 2022, majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya da ta dawo amfani da tsabar kudi a matsayin kudiri na doka tare da ba da tabbacin cewa za su tabbatar da Bankuna sun bi doka. Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Muda Umar mai wakiltan Bauchi ya gabatar a zaman majalisar, inji rahoton Businessday.
A cewar majalisar a ranar 28 ga watan Fabrairun 2007, Najeriya ta kashe makudan kudade wajen bullo da amfani da tsabar kudi karkashin gyaran tattalin arziki wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi ya yi.

Gwamnatin tarayya tana kashe makudan kudade wajen samar da kwabbai
Ya bayyana cewa an sake samfurin takardun kudi na N50, N20, N10 da N5 an yi musu sabbin zubi hakazalika,kwabo N1 da kobo 50, yayin da aka kirkiro da sabon tsabar kudi N2.
Umar ya yi mamakin bayan makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya ta kashe wajen samar da sulalla a matsayin wani bangare na kudin da doka ta tanada, ace babu su a yanzu inji Dailytrust.

Abin da Umar ya ce:

Ayyukan kasuwanci na yau da kullum da mutanen Najeriya ke yi ya samu tangarda, saboda rashin amfani da kudin sulalla da sauran kananun kudi hakan ya haifar da hauhawar farashi zuwa Naira mafi kusa, lamarin da za a iya kwatanta shi a matsayin hauhawar farashin kayayyaki ta fuskar tattalin arziki.
Na Damu kwarai ganin yadda wasu kasashe ke amfani da sulalla wajen hada-hadar kudaden su na yau da kullun,amma mu a nan Najeriya kudade irin su kwabo 50, N1 da N2 duk an daina amfani da su.

Arziƙin Dangote ya ƙaru da N1.5bn sa’o’i kaɗan bayan buɗe kamfanin takin sa
Ranar Talata 22 ga watan Maris na shekarar 2022, rana ce ta farin ciki ga Aliko Dangote wanda yafi kowa arziƙi a nahiyar Afrika.
Sa’o’i kaɗan bayan ya buɗe kamfanin sa na taki mai girman ton miliyan uku akan kuɗi dala biliyan 2.5 ($2.5bn), wata sabuwar ƙididdiga daga Bloomberg ta nuna cewa arziƙin Dangote ya ƙaru da naira biliyan 1.5 (N1.5bn) a cikin sa’o’i kaɗan. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Kamfanin takin na Dangote na zuwa ne a daidai lokacin da yaƙin ƙasashen Rasha da Ukraine ya sanya farashin iskar gas ya ƙaru wanda shine sinadarin da ake haɗa Urea.
Reuters ta rahoto cewa a yayin ƙaddamar da kamfanin wanda shugaban ƙasanMuhammadu Buhari yayi, Dangote ya bayyana cewa zaa rinƙa fitar da takin zuwa ƙasar Brazil, Amurka, India da kuma Mexico.

Kamfanin yana nan a rukunin sashin kasuwanci na Lekki Free Zone a jihar Legas. Kamfanin zai dinga samar da taki ga kasuwanni da dama a nahiyar Afrika.
Sai dai ba Dangote ne kawai ba, shi ma kamfanin Notore-agro-allied and chemicals business wanda ya ke a jihar Rivers, yana da ƙarfin samar da taki ton 500,000 a shekara.

Akwai kuma kamfanin ƴan ƙasar Singapore wato Indorama Eleme Petrochemicals Ltd, wanda ya shirya ninka abinda ya ke samarwa na takin urea zuwa ton miliyan 2.8.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe