24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Tsufa ya zo da gardama: Kotu ta gurfanar da tsohon da ya tafka damfarar N20.7m

LabaraiTsufa ya zo da gardama: Kotu ta gurfanar da tsohon da ya tafka damfarar N20.7m

An gurfanar da wani dattijo Fasasi Adebambo, a gaban wata babbar kotun Legas jiya bisa laifin damfarar naira miliyan N20.7 (N20.7m)

An miƙa dattijon gaban alƙali

Adebambo, mai shekaru 84, an miƙa shi gaban alƙaliwa Akintayo Aluko tare da wani Ojobaro Kayode bisa zargin aikata zamba cikin aminci. Jaridar The Nation ta rahoto


Sashin ‘yan sanda na Police Special Fraud Unit (PSFU), wanda ya miƙa waɗanda ake zargin, ya tuhume su da cewa sun amshi kuɗaɗen ne a wajen Dr. Mbeledogu da matarsa akan cewa za su sayar musu da wani gida a yankin Maryland a jihar Legas.

Mai shigar da ƙara na PSFU, Henry Obiaze, ya faɗawa kotu cewa waɗanda ake zargin sun tafka wannan aika-aikar ne tsakanin watan Janairu da Fabrairun 2020.

Ya bayyanawa kotu cewa laifukan da su ka aikata sun saɓawa sashin doka na 8 (a) da 1(1)(a) na hana aikata damfara da sauran laifuka makamantan su na shekarar 2006. Sannan kuma abin hukuntawa ne a sashi na 3 na cikin dokar.

Sun ƙi amsa aikata laifin

Waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Bayan sun musanta aikata laifukan, mai shigar da ƙara ya nemi kotu da ta sanya ranar fara shari’a sannan ya buƙaci kotu da ta sakaya su a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

Kano: Yadda kotu ta sakaya Ado a gidan yari akan satar dunkulen Maggi

Wata kotu da ke zama a Jihar Kano ta sakaya wani mutum mai shekaru 37 a gidan gyaran hali akan satar katan din dunkulen maggi, LIB ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Yusha’u Ado, mazaunin Goron Dutse Quarters ne da ke Kano, kuma yanzu haka ana zargin sa da cin amana tare da cuta.

Tun farko, mai gabatar da kara, Sifeta Abdullahi Wada ya sanar da kotu yadda Jamilu Ibrahi na Galadanci Quarters ya kai korafi ofishin ‘yan sanda da ke Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Sifeta Wada ya ce ya yarda da Ado ta hanyar ajiye katan 260 na dunkulen maggi a shagon sa, bayan ya je kwashe magginsa ya ga katan 22 na maggi mai kimar N216,000 ya yi layar zana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe