24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Hukumomin Saudiyya sun ƙwace jabun ruwan zam-zam kimanin katan ɗari huɗu a Makkah

LabaraiHukumomin Saudiyya sun ƙwace jabun ruwan zam-zam kimanin katan ɗari huɗu a Makkah

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kafafen yada labarai na kasar Saudiyya suka rawaito cewa hukumomi a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya sun ƙwace fakitin Zam-zam sama da 400 wadanda ake zargin na jabu ne kuma ba za a iya sha ba.

A cewar jami’an birnin, an adana kwalaben a cikin yanayin da bai dace da ka’idoji ba kuma sun keta ka’idojin tsabta. An kuma bayyana cewa an cika kwalaben da ruwan da ba a san asalinsa ba kuma an yi wa ruwan lakabi da ruwan zamzam.

Zamzam
Hukumomin Saudiyya sun ƙwace jabun ruwan zam-zam kimanin katan ɗari huɗu a Makkah

Amma an yi sa’a, hukumomin birnin a Saudiyya sun yi nasarar gano su tare da lalata su kafin su yaɗa su tare da sayar da su a kasuwannin gida. Za a ɗauki tsauraran matakan shari’a a kan wadanda suka keta dokar don hana faruwar irin wannan lamari.

A baya-bayan nan ne hukumomin Saudiyya a birnin Makkah suka ƙara yawan ayyukan sa ido a shirye-shiryen azumin watan Ramadan da ake sa ran za a fara a ranar 2 ga watan Afrilun wannan shekara.

Buƙatar samun ruwan zam-zam a cikin watan Ramadan a kan fuskanci ƙaruwarsa sosai. Azumin watan Ramadan wanda ya kasance lokacin ƙololuwar lokacin Umrah da hajji ƙarama ne, alhazai na ƙasashen waje ke amfani da su wajen sayen ruwan zam-zam da yawa don bayar da ruwa mai tsarki a matsayin kyauta ga ‘yan uwa da abokan arziki bayan sun dawo gida.

Wannan kasuwa mai matukar fa’ida, ɓangarori da dama na amfani da ita wajen yin sana’ar haram, wato ta hanyar haɗa ruwan zam-zam da ruwan ma’adinai na yau da kullun.

Tun shekaru da dama da suka wuce gwamnatin Saudiyya ta gargaɗi alhazai da masu aikin Umrah da kada su sayi zam-zam na kwalabe daga masu sayarwa a tituna da shagunan da ba su da lasisi don gujewa kayayyakin jabu.

Haka kuma gwamnati ta kara yin kokarin ganin an dakile bakar kasuwar ruwan Zam-zam a yankin. Ana yin haka ne domin alhazai sun samu ruwan Zam-zam tsantsa.

Gwamnati ta aiwatar da ka’idoji ta hanyar ba da izini kawai shagunan da aka ba su izinin sayar da ruwan Zam-zam ne za su sayar da shi. Sai dai gwamnatin Saudiyya ta ba da izini ga Kamfanin Ruwa na ƙasa (NWC) ya raba ruwan Zam-zam, wanda ya kai lita biyar ga kowanne mahajjaci daidai da kayan da aka bari a cikin jirgin.

Kamfanin Raja Abdullah na Zam-zam Water Project ne ya gudanar da tattara kayan. A kullum, wannan kamfani yana samar da zam-zam cubic 5,000 da kuma kwalaben roba dubu 200 mai ɗauke da lita biyar na ruwa.

Wasu ‘yan biyu yaya da Kani sun yi wa mahaifiyarsu kisan gilla a birnin Riyadh na kasar Saudiyya

Wasu ‘yan biyu da suka kashe mahaifiyarsu kuma suka ji wa babansu da wani ‘dan uwan su rauni, suna daga cikin mutane 81 wadanda aka zartarwa da hukuncin kisan da kasar Saudiyya ta yi a makon da ya gabata.. 

Yadda ‘yan biyun suka aiwatar da ta’addancin kisan


A watan Yulin shekarar 2016 ne ‘yan biyun suka ja tsohuwar mahaifiyar tasu ‘yar shekara 67 zuwa dakin ajiya inda suka dinga yankar ta da wuka babu kakkautawa a Saudiyya.


Bayan haka, sai suka koma kan Mahaifin su mai shekara 73 wanda yake a wani bangare a cikin gidan, inda shima suka caccaka masa wuka. Bayan sun gama da uban sai suka fafaro kaninsu ‘dan shekara 22 shima suka yayyanke shi da wuka. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe