22.9 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Kaka Ta tafi Kaka Ta Dawo: Bidiyo da Hotunan yadda wata jaririya ta yamutse fuska bayan ta tashi a bacci ya ba da mamaki

LabaraiKaka Ta tafi Kaka Ta Dawo: Bidiyo da Hotunan yadda wata jaririya ta yamutse fuska bayan ta tashi a bacci ya ba da mamaki
35fb5c4e05174bfd
Bidiyo da hotuna wata jaririya ta yamutse fuska bayan ta tashi a bacci

Jarirya ta bata fuska tana kallon dai-dai bayan tashin ta daga bacci

Wani faifan bidiyo mai ban al’ajabi da ban dariya na wata jaririya ‘yar Najeriya data yamutse fuska ya jefa masu amfani da shafukan sada zumunta cikin mamaki. Gajeren bidiyon da @yabalefonline ya yada a Instagram ya nuna yadda jaririyar ta tashi a bacci cikin kwanciyar hankali.
Ko da jaririyar ta bude idonta ta juya tana kalle kalle nadan wani lokaci kafin nan ta maida kanta ta yamutse fuska, kamar wacce aka aiko wa da sakon mutuwa.
Hakan da ‘jaririyar ta yi ya bar mutane da sakin baki a yayinda ahalinta suka tsunduma tunanin kodai kakar su data mutu ne ta dawo!.

Mutane sun cika da al’ajabin wannan jaririya

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun sha mamakin wannan abu ,ga kadan daga cikin martanin su:

bekeebaby419 ta ce: “Yarinyar tana mamaki ne irin “Kuna nufin ku ce a Najeriya na ke ko Seun whyne mi ni?”

@zeenodavid ya ce: “ta fahimci cewa duk yawan kasashen da a ake da su a duniya arasa inda za a haifeta, sai Najeriya ..”
@esther_unbuthered ta ce: “Idan na sami wannan jaririyar zan mata wanka da bokitin magani.”

@i_f_e_c_h_u_k_w_u_d_e ta ce: ” idan an gaya muku ku yi amfani da kariya, ba za ku yarda ku yi ba yanzu gashi kunsa na sake dawowa cikin wannan jahannama da ake kira Najeriya.”

@ayoksofficial ta ce: “yarinya ta gama sa rai za a haifeta a Maryland Amurka,kawai kuka haife ta a Maryland Palm Groove…”

Yadda na yi dakon jaki a ciki na tsawon shekaru 2, inji Talatu, matar da ta haifi jaki a Zaria
ranar Talata, labarin Murja, wacce aka fi sani da Talatu ya bazu a cikin garin Tudun wada da ke karkashin karamar hukumar Zaria, Jihar Kaduna akan yadda ta haifi jaki, maimakon jinjiri.

Mutane da dama sun yi tunanin doki ne, sai dai da bakinta ta tabbatar wa wakilin LabarunHausa.com cewa jaki ne ba dokin ba.
Wakilin labarunHausa.com ya samu damar zuwa har gidan da ta ke zama a Layin Lemu, nan cikin Tudun Wadan Zaria, har ya tattauna da ita akan lamarin mai firgitarwa.

Kamar yadda ta bayyana, ta yadda da hakan a matsayin kaddarar ta kuma asiri ne wanda aka yi mata tun daga daukar cikin yayayyar yarinyar ta.
A cewar Talatu:

“Na je asibitin dafta Umar inda ya duba ni bai ga komai ba. An yi min hoto amma sai likitan ya ce ruwa kadai yake gani. Magunguna dai iri-iri duk da kasancewa ta ba mai karfi ba.”

Ta shaida yadda ta samu labarin wata mata da ke Kano mai magani irin na Islamic Chemist kuma ba ta da kudi. Sai dai ta samu rance tukunna bayan matar ya zo Zaria ta duba ta har ta ce akwai ajiya a jikin ta.

Bayan yi mata addu’o’i da ba ta magunguna, sai ta haifi wannan jaririn jakin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe