27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Mun kara farashi ga kwastomomin mu saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasa, Kungiyar Karuwai

LabaraiMun kara farashi ga kwastomomin mu saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasa, Kungiyar Karuwai

Wata kungiyar karuwai da ke Accra, kasar Ghana ta bayar da sanarwa dangane da yadda farashin aikin su ya karu, LIB ta ruwaito.

A cewar kungiyar, tabarbarewar tattalin arziki tare da tsadar man fetur ne yasa wajibi suka kara tsadar aikin na su.

karuwai
Mun kara farashi ga kwastomomin mu saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasa, Kungiyar Karuwai

Yanzu haka, wajibi ne kwastoma ya dinga biyan tsakanin $50 zuwa $300, kuma kada ya kuskura ya wuce mintina 15 zuwa 20.

Har ila yau, wajibi ne kwastoma ya lale $300 ya biya idan hara yana da niyyar kwana.

JoyNews ta ruwaito yadda karuwan suka bukaci kwastomomin su akan su kara hakuri dangane da karin farashin.

An cafke wata mata da ta mayar da gidanta gidan karuwai a Zaria

Wata mata mai ‘ya’ya biyu, mai suna Altine Abdullahi, ta bayyana a gaban babbar kotun majistire dake unguwar Kofar Fada a garin Zaria, ranar Talata 31 ga watan Agusta, bisa zargin mayar da gidanta gidan karuwai.

Rundunar ‘yan sanda na tuhumar Altine da wani mai suna Muhammad Yasir da laifin hada baki, yada alfasha, sace mutane, wanda ya sabawa sashe 59, 230 da kuma sashe na 368 na sharia.

Dan sandan da ya gurfanar da masu laifin, Insp. Abdullahi Sarki, ya sanar da kotu cewa ‘yan sanda tuni sun kammala bincike akan wannan lamari, kuma a shirye take su cigaba da shari’ar.

Sai dai kuma, alkalin kotun, Zainab Garba, ta bukaci sashen binciken manyan laifuka ta CID dake Kaduna da ta cigaba da bincike akan lamarin.

A cikin rahoto na farko da aka fara fitarwa, masu shigar da karar sun bayyana cewa a ranar 10 ga watan Agusta da misalin karfe 1 na rana, Bello Shehu da yake zaune a gida mai lamba 97 dake unguwar Rimin Doko, Zaria, ya kai karar cewa Yasir ya kai diyar shi mai shekaru 15 wacce aka boye sunanta zuwa gidan Altine dake unguwar Gwargwaje Zaria.

Haka kuma masu shigar da karar sun bayyana cewa Altine ta bawa Yasir daki, inda ya biya naira dubu daya (N1,000), haka ya kwanta da yarinyar kuma ya yi mata ciki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe