27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Yadda na yi dakon jaki a ciki na tsawon shekaru 2, inji Talatu, matar da ta haifi jaki a Zaria

LabaraiYadda na yi dakon jaki a ciki na tsawon shekaru 2, inji Talatu, matar da ta haifi jaki a Zaria

A ranar Talata, labarin Murja, wacce aka fi sani da Talatu ya bazu a cikin garin Tudun wada da ke karkashin karamar hukumar Zaria, Jihar Kaduna akan yadda ta haifi jaki, maimakon jinjiri.

Mutane da dama sun yi tunanin doki ne, sai dai da bakinta ta tabbatar wa wakilin LabarunHausa.com cewa jaki ne ba dokin ba.

Wakilin labarunHausa.com ya samu damar zuwa har gidan da ta ke zama a Layin Lemu, nan cikin Tudun Wadan Zaria, har ya tattauna da ita akan lamarin mai firgitarwa.

Kamar yadda ta bayyana, ta yadda da hakan a matsayin kaddarar ta kuma asiri ne wanda aka yi mata tun daga daukar cikin yayayyar yarinyar ta.

Kamar yadda ta shaida, bayan haihuwar diyar ta karama, kasancewar yaranta 11 a duniya, ta ke fuskantar ciwo matsananci.

A cewar Talatu:

“Na je asibitin dafta Umar inda ya duba ni bai ga komai ba. An yi min hoto amma sai likitan ya ce ruwa kadai yake gani. Magunguna dai iri-iri duk da kasancewa ta ba mai karfi ba.”

Ta shaida yadda ta samu labarin wata mata da ke Kano mai magani irin na Islamic Chemist kuma ba ta da kudi. Sai dai ta samu rance tukunna bayan matar ya zo Zaria ta duba ta har ta ce akwai ajiya a jikin ta.

Bayan yi mata addu’o’i da ba ta magunguna, sai ta haifi wannan jaririn jakin.

A cewar ta:

“Cikin ikon Allah sai ga jinjirin jaki na haifa. Lamarin da ya firgitar da duk makwabta da masu kallo.”

Ta bayyana yadda yanzu haka ta samu lafiya don a baya ko tafiya ta nemi ta gagare ta. Tana yawan jin motsin abu a cikin ta, ashe ga abinda aka tura mata.

Talatu ta yi kira ga mata akan su kasance masu tsoron Allah akan harkokin su na yau da kullum. Don a yadda ta fadi, wata ce wacce ba ta sani ba ta tura mata bakaken aljanu har suka yi mata wannan aika-aikar.

Yayin da aka tambaye ta idan tana bukatar tallafi, ta ce tabbas tana bukata don mijin ta ba mazauni bane, almajiri ne mai nema.

Ta kasance tana sana’a, sai dai zara bata barin dami. Ta nemi taimako daga ‘yan Najeriya masu hannu da shuni da kuma gwamnati akan a taimaka mata wurin samun gida, don a gidan haya take wanda shi ma sau dayawa kudin hayar yana gagara.

Mutane da dama sun tausaya wa rayuwar ta, inda suka bukaci a ceto ta daga wannan yanayi da ta samu kan ta.

Allahu Akbar: Bidiyon dokin da wata mata ta haifa a garin Zaria

A duk lokacin da aka kira Allah, Ubangiji mahalicci, dole mutum ya yarda da cewa shi ne mai yin komai da kuma kowa.

A ranar Talata, 21 ga watan Maris na shekarar 2022 da yamma labarin yadda wata mata ta haifi wata halitta mai kama da doki ya bazu a garin Zaria cikin Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a layin Lemu da ke Tudun wadan Zaria kamar yadda ganau suka shaida wa wakilin Labarun Hausa.

Bayan isa gidan da lamarin mai ban al’ajabi ya faru, wakilin Labarun Hausa bai samu damar ganawa da matar da ta haifi jaririn dokin ba, amma ya gan ta kuma makwabtan ta sun tabbatar masa da hakan.

Anan ne ma wakilin namu ya samu bidiyon halittar mai kama da doki wanda tuni ya fara bazuwa a shafukan sada zumunta.

Mutanen gidan sun bayyana yadda aka birne halittar kasancewar abu ne mai ban tsoro da kuma mamaki ace dan adam ya haifi dabba.

Ku ci gaba da kasancewa tare da mu, nan ba da jimawa ba, zamu kawo muku cikakken bayani akan yadda wannan lamari mai firgitarwa ya faru.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe