24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wani dalibin Yukirain dan Najeriya ya mutu a sakkwato,  sati biyu kacal bayan an tseratar dasu

LabaraiWani dalibin Yukirain dan Najeriya ya mutu a sakkwato,  sati biyu kacal bayan an tseratar dasu


 Wani dalibi dan Najeriya mai suna Uzaifa Halilu Modachi, da yake karatu a kasar Yukirain ya mutu, a garin Sokoto, sati biyu kacal bayan dawowar sa Najeriya. 


Kafin rasuwar sa Halilu Modachin, ya zauna a kasar Yukirain din tsawon shekara uku ba tare da ya dawo hutu gida Najeriya ba. 


Dan shekarar karshe a karatun sa, a jami’ar lafiya ta Zaporozhye, yana kan shirin fara jarrabawar karshe ne yaki ya barke tsakanin Yukirain din da kasar Rasha. 


Jawabin mahaifin Dalibin bayan rasuwarsa

dalibi
Uzaifa Halilu Modachi dalibin Yukirain dan Najeriya da ya mutu bayan dawowa gida Najeriya

Da yake bayyana alhininsa, baban mamacin honarabul Habibu Haliru Modachi, dan majalisa a jihar Sokoto, yace :

” Alhandulillah, Allah shine ya bayar da rayuwa , kuma ya karbi abarsa, haka ya tsara abin sa kuma bamu da ja akan hakan” 


“Da ace a kasar Yukirain ya rasu, sai an fadi abubuwa da yawa akan sa, ko ace sojojin Rasha ne suka kashe shi, ko ace yayi hadari, ko kuma ace sojin Yukirain ne suka harbe shi. 

” Muna matukar godiya ga Allah da ya sanya ya mutu a gabanmu, muna kuma matukar godiya ga gwamnati, musamman ta jihar Sokoto, saboda kokarin tseratar dasu da tayi tun kafin rincabewar yakin na Yukirain. “

Yan bindiga sun sace mutum 9 ciki har da dalibin sakandare a Katsina

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani sabon hari garin Albasun Liman dake cikin karamar hukumar Sabuwa cikin jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da mutane tara.

Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din akwai dalibin makarantar sakandare wanda yake ajin kusa da karshe a makarantar sakandare ta Damari, wanda aka bayyana sunanshi da Umar Mu’awiya, tare da mahaifinsa.

A cewar mazauna garin, ‘yan bindigar sun kai wannan hari ne a daren ranar Laraba 30 ga watan Disamba da misalin karfe 12:30 na dare. Rahoton jaridar PUNCH.

Idan ba a manta ba a ranar bikin Kirsimeti, mutum takwas da aka sace inda cikinsu hadda ango da amaryarsa sun samu sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar a yayin da ‘yan bindigar ke bacci.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, domin tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa za su gabatar da bincike akan wannan lamari.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe