35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ba ina nufin duka larabawa ne keda wariyar launin fata ba cewar Shahida diyar Sunusi Lamido

LabaraiBa ina nufin duka larabawa ne keda wariyar launin fata ba cewar Shahida diyar Sunusi Lamido
Shahida Sanusi
Ba ina nufin duka larabawa ne keda wariyar launin fata ba inji shahida diyar Sunusi Lamido

Shahida sunusi ta ce ba a fahimci maganar ta bane

A cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram, diyar tsohon sarkin Kano Sunusi ta yi karin haske kan wasu kalamai da ta yi tun farko dangane da yadda ta fuskanci wariyar launin fata a kasar Saudiyya, inda a halin yanzu take zaune tare da mijinta.
Shahida ta amsa tambayar da aka yi mata kan ko ta taba fuskantar wariyar launin fata a Kasar Saudiyya, inda ta ce eh, “har a cikin masallaci da filin wasan da ke gaban gidanmu”.

sannan ta ba da labarin yadda aka taba cin zarafin ‘yarta wadda ta kasance “daya daga cikin baƙar fata biyu da suke makaranta ”,kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a baya.

Cikin sa’o’i kadan karamar magana nason zama babba

Shahida ta ce ta yi mamakin yadda wata magana da ta yi a baya ya janyo cece kuce na tsawon lokaci.
Ta ce ba wai tana nufin duka Larabawa ne keda halin wariyar launin fata ba, inda ta kara da cewa tana da kawaye Larabawa,tace maganar da ta yi ba a fahimce ta ba ne.
“Na yi mamakin yadda labarin ya jawo sharhi sosoi a Instagram saboda banyi tsammanin zai wuce sa’o’i 24 ba, amma sai gashi ya zaga ko ina ya zama abin magana a yanar gizo. Don haka zan yi karin bayani tare da bada hakuri. Ina neman afuwar duk wanda abin ya shafa ko bai ji dadin maganar ba..

Ba ina nufin duka Larabawa ne su ke da wariyar launin fata ba, ba haka lamarin yake ba. Ina da kawaye Larabawa. Kuma duk da akwai mutanen da ba bazan kira su da kawaye na ba amma kuma ba zan aiban ta su ba mutanen kirki ne, na yi kuskuren furuci ne.

Rashin bayani shi ya haddasa cece kuce

Na yi magana game da abubuwan da suka faru na wariyar launin fata amma ban yi bayani sosai a kan su ba, a gaskiya: a makarantar diya ta daya daga cikin ma’aikatan wurin ne kawai ke da wariya kuma hakan ya faru shekaru 2 da suka wuce bata dade ba tabar makarantar. Ban taba kawo karan ta ba saboda nasan babu wata hulda sosai tsakanin mu da ita ina tsammanin makarantar ta lura da wani abu game da ita wanda hakan ya janyo suka sallami malamar.
A gaskiya, kamar yadda na bayyana a baya, ba wai na fuskanci wariyar launin fata kai tsaye ba ne yawanci ana yin abu da muke ganin sa kamar wariyar launin fata. Don haka watakila wannan ba da wata manufa aka yi ba. Kasar Saudiyya kasa ce da ke kunshe da mutane daban daban kuma da yawa daga cikin larabawan da ake mu’amala da su a nan ba ‘yan asalin kasar Saudiyya ba,ne.watakila ba ma Larabawa ba ne.

Ina kara bada hakuri Na gode da fahimtar ku, ” sakon shahida ya bayyana.

Yan kudu sun hau fargaba akan ko dai Genevieve ta musulunta bayan ta yi wallafa da ayar Qur’ani, dadduma da kabari
Jarumar masana’antar fina-finan kudu, Genevieve Nnaji ta saki wani gajeren bidiyo a shafin ta na Instagram ya tayar da kura inda aka dinga musayar ra’ayi dangane da bidiyon, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gajeren bidiyon ya nuna tunatarwa ne akan cewa duniyar nan ba komai bace ba a harshen turanci.
A bidiyon an nuna cewa lahira ce tabbatacciya kuma komai na duniyar nan mafalki ne ba gaskiya ba.

Bidiyon ya nusar da mutane akan su farka, kuma an sanya ayar Al’Qur’ani mai girma da kuma dadduma.

Kamar yadda ake fadi a cikin bidiyon:

“Don Allah! Don Allah! Ku farka! Ku farka! Ku farka! Ko wanne mai rai mamaci ne.”
Bayan ta wallafa bidiyon nan, ya zama abin surutu da kuma fargaba, inda masoyanta musamman ‘yan kudu suka hau cece-kuce.
Sun yi fargaba akan kada fa ace jarumar nan ta musulunta ko kuma shirin musulunta take yi, idan ba haka ba, tana kirista, mai zai hada ta da wallafa ayar Qur’ani, dadduma ko kuma makabarta?

Duk da dai a bangaren story ta wallafa bidiyon kuma bayan awa daya story ke bata a Instagram. Amma sai wata ma’abociya instagram mai suna poshjournal ta kwafo kuma ta wallafa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe