24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wata mata ta cinnawa ‘yar cikin ta wuta da man fetur

LabaraiWata mata ta cinnawa 'yar cikin ta wuta da man fetur

Wata mata mai suna Aisha Tijani ta shiga hannun jami’an ‘yan sandan jihar Ogun bayan ta cinnawa ‘yar cikin ta mai shekaru goma a duniya wuta. Jaridar Tribune ta rahoto

An bayyana inda lamarin ya auku

Lamarin a cewar kakakin ‘yan sandan jihar, Abimbola Ayeyemi, ya auku ranar Lahadin da ta gabata a yankin Mowe cikin ƙaramar hukumar Obafemi-Owode ta jihar.

An kai rahoto wurin ‘yan sanda

Wata mata mai suna Moroof Ayinde wacce su ke zaune gida ɗaya da Aisha Tijjani ita ce ta kai rahoton lamarin a gaban ofishin ‘yan sanda na Mowe. Ta bayyana wa ‘yan sanda cewa wacce ake zargin ta fusata ne bayan yarinyar ta bayar da wayar da aka ƙwace a hannun ƙannen ta.

DPO ɗin Mowe, CSP Folashade Tanaruno, bayan samun bayanai, ya tura jami’an sa zuwa inda lamarin ya auku domin cafke wacce ake zargin.

Yarinyar ta samu munanan raunika

DSP Oyeyemi, ya bayyana cewa yarinyar ra samu mummunar ƙona inda aka garzaya da ita zuwa asibitin koyon kiwon lafiya na Olabisi Onabanjo University Teaching Hospital (OOUTH), a Sagamu.

A lokacin da ake gudanar da bincike, matar wacce tayi iƙirarin sun rabu da mahaifin yaran, ta bayyana wa ‘yan sanda cewa ba ta san abinda ya faru da ita ba yayin da ta ke aikata wannan mummunan aikin.

Yan sanda sun cafke wata mata wacce ta ƙona ɗuwawun ɗiyar mijinta da wuƙa mai zafi

‘Yan sandan jihar Bayelsa sun cafke wata mata mai suna Esther Otoniye, bisa laifin ƙona ɗuwawun ɗiyar mijin ta mai shekaru 10 da wuƙa mai zafi.

Otinoye wacce aka cafke a gidan su da ke Akenfa wajen birnin Yenagoa, babban birnin jihar, ta bayyana cewa ƙaramar yarinyar ta sharara mata ƙarya ne. Jaridar Independent.ng ta rahoto.

Jikin ƙaramar yarinyar yasha tabbai sosai waɗanda aka zargin ta same su ne ta hanyar shan bugu sosai.

‘Yan sanda sun ɗamƙe matar

An samo cewa a ranar Asabar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ben Okolo, ya bayar da umurnin cafke Otinoye bayan wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin mata da ƙananun yara sun shigar da ƙorafe-ƙorafe a kan ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe