24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Arziƙin Dangote ya ƙaru da N1.5bn sa’o’i kaɗan bayan buɗe kamfanin takin sa

LabaraiArziƙin Dangote ya ƙaru da N1.5bn sa'o'i kaɗan bayan buɗe kamfanin takin sa

Ranar Talata 22 ga watan Maris na shekarar 2022, rana ce ta farin ciki ga Aliko Dangote wanda yafi kowa arziƙi a nahiyar Afrika.

Arziƙin Dangote ya ƙaru

Sa’o’i kaɗan bayan ya buɗe kamfanin sa na taki mai girman ton miliyan uku akan kuɗi dala biliyan 2.5 ($2.5bn), wata sabuwar ƙididdiga daga Bloomberg ta nuna cewa arziƙin Dangote ya ƙaru da naira biliyan 1.5 (N1.5bn) a cikin sa’o’i kaɗan. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Kamfanin takin na Dangote na zuwa ne a daidai lokacin da yaƙin ƙasashen Rasha da Ukraine ya sanya farashin iskar gas ya ƙaru wanda shine sinadarin da ake haɗa Urea.

be8daaf5104a8b94
Ma’aikata a rukunin kamfanin taki ds tatar mai na Dangote. Hoto daga Legit.ng

An bayyana ƙasashen da zaa kai takin

Reuters ta rahoto cewa a yayin ƙaddamar da kamfanin wanda shugaban ƙasanMuhammadu Buhari yayi, Dangote ya bayyana cewa zaa rinƙa fitar da takin zuwa ƙasar Brazil, Amurka, India da kuma Mexico.

Kamfanin yana nan a rukunin sashin kasuwanci na Lekki Free Zone a jihar Legas. Kamfanin zai dinga samar da taki ga kasuwanni da dama a nahiyar Afrika.

Yayin da babban bankin Najeriya ya dakatar da amfani da canjin kuɗin sa wajen shigo da taki domin ƙarfafa yin takin a cikin gida, hakan na nufin cewa manoman Najeriya za su dogara sosai ga kamfanin takin na Dangote.

Dangote na da abokan takara

Sai dai ba Dangote ne kawai ba, shi ma kamfanin Notore-agro-allied and chemicals business wanda ya ke a jihar Rivers, yana da ƙarfin samar da taki ton 500,000 a shekara.

Akwai kuma kamfanin ƴan ƙasar Singapore wato Indorama Eleme Petrochemicals Ltd, wanda ya shirya ninka abinda ya ke samarwa na takin urea zuwa ton miliyan 2.8

Dangote ya yi wa Elon Musk da Bill Gates zarra a cikin sa’o’i 24, arzikinsa ya hauhawa fiye da nasu

Attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Aliko Dangote, a cikin sa’o’i 24 da suka wuce, ya samu karuwar arziki da kimanin Naira biliyan 28.86 (dala miliyan 69.4).

A cewar Bloomberg, kudin Dangote ya kai kimanin dala biliyan 20 a yanzu, wanda hakan ya sa ya zama na 83 a cikin jerin masu arziki yayin da ya farfado daga asarar da ya samu a makon jiya.


Tun farkon shekarar 2022, arzikin Dangote ya hauhawa da dala miliyan 934 (N388.5bn) sakamakon yadda kamfanin simintinsa ya samu karbuwa sosai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe