29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Na wanke wa jarumai mata bireziyya da dan pant, inji Jarumi Mustapha Naburaska

LabaraiKannywoodNa wanke wa jarumai mata bireziyya da dan pant, inji Jarumi Mustapha Naburaska

Fitaccen jarumin barkwanci, Mustapha Naburaska ya bayyana a irin wahalhalun da ya sha a masana’antar Kannywood kafin ya kai wannan matakin da yake a yanzu a wata hira da Arewa 24 ta yi da shi a cikin shirin Gari ya waye inda ya amsa tambayoyi da dama.

A cikin hirar, Naburaska ya bayyana cewa a baya ba ya da wata daraja a masana’antar Kannywood sai dai a aike shi siyo sigari, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

nabraska 2
Na wanke wa jarumai mata bireziyya da dan pant, inji Jarumi Mustapha Naburaska

Ya ci gaba da bayyana cewa har wankin bireziyya da dan pant ya yi wa manyan jarumai mata. Ya ce har rikon jaka ya yi musu a lokacin ba ya da wata daukaka.

A cikin bayanin da jarumin ya yi, ya bayyana yadda ake je da shi don sanya shi cikin waka, inda mashiryin shiri Rabi’u Ibrahim ya wulakanta shi.

A cewarsa, ya ce shi bai ga jarumin da za a sanya a wakar ba. Dama manyan jarumai suna bayar da labarin yadda masu shirya shiri suke raina musu wayau tare da wulakanta su.

Yanzu haka da yawan su sun zama manyan jarumai, shi kuma furodusan yana nan babu wanda ya san da shi a yanzu kuma ya ma bar harkar fim din.

Kamar yadda ya kada baki ya ce:

“Duk sanda na zo, a lokacin iya sigari nake da kimar zuwa in je in siyo. Na yi dan aike, na zo a cikin jaruman mu mata, tsofaffin mata na yi musu wanki da guga.

“Na wanke pant, na wanke bireziyya na tsofaffin jarumai. Na yi rikon jaka ta wata fitacciyar jaruma babba wacce ka san ta na san ta.

“Bayan nan aka zo aka ce za a yi wata waka ta wani babban darekta na lokacin nan sunan shi Rabiu Ibrahim HRB. Wannan jarumar ta tafi da ni ta ce tana rokon alfarma, shi ma wannan a ba shi kaya ya sa.

“Sai ya ce Allah ya kiyaye, ni ban san inda zan sanya wannan ma ya yi acting ba.”

A yanzu haka dai, Mustapha Naburaska ya samu daukaka baya ga nasarorin da ya samu a harkar Kannywood, ya gina gida, ya je makka, ya yi aure kuma ya sake kuma ya sai mota ya kuma samu duk wani rufin asiri da duk wani jarumi yake fatan samu.

Baya ga hakan, kwan nan gwamnan Jihar Kano ya nada shi a matsayin mai ba shi shawarwari na musamman a kan harkar Propaganda. Wadancan wahalhalun da ya sha sun zama labari.

Da fatan Allah ya kara rufa asiri. Ameen ya Allah.

Jarumin Kannywood, Naburaska ya fitar da ‘yan gidan yari 33, ya ce yana so suyi azumi a gidajen su

Fitaccen jarumi mai wasan barkwancin nan na kannywood, Mustapha Badamasi wanda akafi sani da Naburaska a masana’antar Kannywood, ya yi kokarin ganin an saki fursunoni 33 dake tsare gidan gyaran hali na Goron Dutse dake jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Fursunonin da ka suka sami ‘yancin kansun sun hada da, maza 31 da mata biyu.

Jarumin ya bayyana yadda ya yanke shawarar sanya farinciki a fuskokin wasu mutane, musamman da azumin watan Ramadana ke karatowa, don kafa misali ga sauran mutanen dake da damar yin hakan.

Ya bayyana yadda yayi hakan da fatan Ubangiji ya masa jagora gami da bashi lada.

“Hakikanin gaskiya, yin azumi a gidan gyaran hali baya da dadi, shiyasa naga hakan na da matukar mahimmanci in samar musu yancin su da ‘yar damar da nike da ita,” a cewar mai wasan barkwancin.

Ya bukaci masu hannu da shuni da kungiyoyi masu jin kan bil’adama su dage wurin ganin sun ceto rayukan mutane da dama da ke rayuwa a gidajen gyaran hali a fadin kasar, saboda yadda suka wasun su suka gaza biyan kudin tara.

Yayin jawabi a maimakon yan gidan yarin da aka saki, Mado Bala ya yi godiya ga jarumin, tare da alkawarin zama mutanen kwarai, duba da irin darasin da suka koya cikin gidan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe