24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Gaskiya ina Bukatar Aure: Wani saurayi ya koka tare da wallafa Bidiyon dakin kwanan sa

LabaraiGaskiya ina Bukatar Aure: Wani saurayi ya koka tare da wallafa Bidiyon dakin kwanan sa
2497577a89091623
Gaskiya ina bukatan matar aure:Wani saurayi ya koka tare da wallafa bidiyon dakin kwanan sa

Wani saurayi ya bayyana yadda yake tsananin bukatar aure

Mabiya shafukan sada zumunta sun mayar da martani game da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda gidan wani saurayi yake a hargitse. Mutumin mai suna @the_scholar1, ya shiga dandalin sada zumunta na Twitter inda ya koka kan yadda yake tsananin bukatar matar aure, tare da wallafa bidiyon irin halin da yake ciki.

Ko gadon sa baya iya gyarawa

Dakin ko da dai babu wadataccen haske amma ya nuna irin hargitsewan da ya yi babu gyara tufafin sa a zube a kasa da sauran kayan tarkace . Gadon baccin sa shima an hange sa babu shimfidi ga takardu a kai da sauran kayayyaki. Ga kuma datti a tare a gefen daki.

Kadan daga cikin ra’ayoyin mutane game da lamari

@AbeniJade ya ce: “Maimakon ka tsaya kana zance .Ka samo mai aikin da zaka dinga biyanta Naira 3000 zuwa 5000 zasu iya lura da tsaftan gidan. Ni dan kasuwa ne bana son gyaran gida..”

@maureen_dammy ta ce: “Ka koyi kintsa wuri …” Ka koyi dabi’ar mayar da duk wani abu inda ka dauke su….. “ka ware rana daya a kowani mako don tsaftace gidan ka.
dan Allah ya ya kake yin bacci a dakin nan! “Ina so in ga yadda bandaki,da kitchen dinka yake …
…”

@Ab_Ishaq ya ce: Horar da kai, a lokacin samartaka na, dakina yana daya daga cikin daki mafi kyau a cikin abokai na.

Zan dinga ba wa mijina Kashi 20 cikin 100 na Albashina domin ya kula da kansa, maza na shan wahala sosai- wata budurwa ta bayyana
Wata budurwa ‘yar Najeriya mai shafin Twitter @A_Blackwoman ta tayar da kura a shafinta na Twitter bayan ta bayyana irin kason da za ta bawa mijinta da ga cikin albashin ta. A cikin sakon da ta wallafa a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, budurwar ta ce hakika nauyi ya yi wa maza je yawa.
Budurwar ta kara da cewa tana son ba wa mijinta kashi 20 na albashin ta a matsayin hanyar tallafa masa, yayin da kashi 30 kuma za su shiga asusun amfanin gida.Ta ce ta na matukar tausayin mazan da ke aiki tukuru musamman masu aikin karfi, ta kara da cewa ta taba haduwa da wani makanike wanda yake kokarin neman na abinci, sai kuma wani mutum mai siyar da kayan lambu a tsakiyar rana.
Ga abinda ta ce:

“…akwai wasu mutane da za ka gan su ,suna kokarin kwantar da hakarkarinsu za su dan huta su sami barci ko na minti daya zuwa biyu a saman siminti, a karkashin rana, mijina ya more,bazan bari ya sha wahala ba.“

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe