22.9 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Wani matukin keke Napep ya dawo da jaka mai dauke da wayoyin hannu 10 ga mai su, bayan ya mantasu a bin hawansa inda aka bashi N1000 ladam tsuntuwa

LabaraiWani matukin keke Napep ya dawo da jaka mai dauke da wayoyin hannu 10 ga mai su, bayan ya mantasu a bin hawansa inda aka bashi N1000 ladam tsuntuwa

Halayyar gaskiya da wani matukin keke napep ya nuna ya taba zukata a yanar gizo, inda aka mai dashi abin yabo. 


Matukin dan Najeriya, ya gano cewa wani fasinja, ya manta wata jakarsa a cikin abin hawansa, wadda take dauke da wayoyi sababbi har guda goma, inda shi kuma ya dauki aniyar zakulo mai kayan. 


A cikin bidiyon da yake yawo, daga karshe ya sami mai kayan inda aka bashi landan Naira dubu daya N1000. 
Wani fasinja ya cika da mamaki, bayan wani mai imanin matukin keke napep ya dawo masa da kayan sa da ya manta a cikin abin hawan nasa. 


 Kafar instagram ta @gossipmilltv  sun nuna wani bidiyo, inda wani mai gaskiyan direban keke, ya sami mai wata jaka dake dauke da sabbin wayoyin hannu guda goma gami da wadansu kayayyaki da ya manta a abin hawan matukin keken. 

matuki
Matukin ya sami ladan tsuntuwa


A fadar matukin mai gaskiya, yace yayi kokarin gano mai asalin mallakin kayan, tun lokacin da ya fuskanci an manta su a abin hawansa, inda daga baya yayi sa’ar gano mai kayan. 


Matukin ya sami ladan tsuntuwa 


Lokacin da mutane ke yabonsa a yayin da yake dankawa mai kayan kayansa, matukin  yana ta murmushi, inda yace, duk da dai shi mashayine; amma bazai taba yin sata ba. 


Legit.ng sun tabbatarda faruwar lamarin a garin Aba, dake jihar Abia, inda aka baiwa matukin Naira dubu daya N1000 a matsayin ladan tsuntuwa. 


 Sharhin yanar gizo 

@hype_frosh yace: 
” Ai mutumin ma bai sami wani kudi da yawa a, to nawa ya samu, dubu daya ne fa kacal da ya sanima da ya tsere, amma dai an gode maka da ka dawo da su dan albarka”. 

@pearl_kemisola08 yace : “Allah ya ma albarka, kai na Allah ne.  Baka saniba ko ta wannan hanyar Allah zai albarkace ka, shi yasa ka dawo da su, Allah shi karo Albarka. Oga oo “

@queenseyyxo yace :” Na san zai koma gida ne ya kasa bacci, ya kasa bacci na dare 40 yana ta tunanin mai yasa ya mayar da tsala-tsalan wayoyi ranar da ya tsince su.” 

@temmiehairlyn yace : ” Bashi Naira dubu daya N1000 fa gaskiya akwai……. Sannan kuma na sami wayoyi har guda 10, kai! gaskiya baka yi ba.”

Wani direba da ya tsinci miliyan daya da dubu dari biyu 1.2m kuma ya mayarwa da mai shi, amma ba’a bashi ko sisi ladan tsuntuwa ba

Wani matashi dan Nageriya Emmanuel Christopher, ya dawo da kudi kimanin dala dubu uku $3,000 daidai da N1,247,520 na kudin Najeriya, wanda wata mata ta manta a matarsa bayan ya dauke ta a matsayin hayar tasi.


Duk da zugar da Shaidan ke yi masa akan ya rike dalolin, amma Emmanuel din yayi abin da ya dace, ya dawo mata da kudinta .

Yan Nageriya da dama sun ji haushin matar mai kudin, saboda bata bashi ko sisi ba na landan tsuntuwa. 


Wani matashi dan Nageriya Emmanuel Christopher, ya sha yabo a kafar sada zumunta, sakamakon makurar gaskiyar sa da ya nuna wajen dawowa da wata fasinjar sa kudadenta da ta manta a motarsa, a Abuja. 

Matar mai suna Wise Lara, wadda ta bayyana irin halin kirkin sa, a shafinta na Facebook, tace shi mutumin dan Cocinsu ne, kuma mutum ne mai matukar jajircewa. 

Daloli, fasko, da kuma sauran abubuwa masu daraja

A fadar ta, tace a lokacin da Emmanuel ya sauke fasinja mace a birnin tayya, can sai ya fahimci kamar ta manta wata jaka mai dan kumari, a kujerar baya. 

Bashi da tabbacin ta waye, kawai sai ya bude jakar, inda yaci karo da daloli, da sauran kudaden kasar waje. 

Ya iya lissafa sama da dala dubu uku $3,000 daidai da kudin Najeriya N1,247,520, da kuma wasu sauran kudaden kasashen waje. Banda ma kudin, dan tasi din ya ga katin ATM guda uku, da kuma fasko na kasashen waje guda uku. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe