22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Wani Magidanci ya zage yana tikar rawa a gaban matar sa da ‘ya’yansa saboda kawai kungyiyar kwallon kafa ta Basalona ta doke Riyal madrid

LabaraiWani Magidanci ya zage yana tikar rawa a gaban matar sa da 'ya'yansa saboda kawai kungyiyar kwallon kafa ta Basalona ta doke Riyal madrid
0ac08944185b047d
Wani magidanci ya zage yana tikar rawa a gaban matar sa ‘ya’yansa saboda kungiyar kwalon kafa ta Basalona ta doke riyal madrid

Murnar cin kwallo yasa wani tsoho taka rawa

Wani dan Najeriya ya yada a shafin sa na twitter yadda mahaifinsa ya yi shagalin murna bayan da kungiyar kwallon kafa ta Basalona ta doke Riyal Madrid a El Clasico. A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, an ga dai magidanci ya zage yana,tikar rawa duk da cewa yana sanye da dan tawul yayin da ya ke rera waka “4-0”. Cikin fari ciki da murna ya ke zungurin matar sa daga inda take zaune a kan kujera.

Iyalan sun kasance cikin farin ciki

‘ya’yansa da ke zaune a bayansa sun zage sai kwasar dariya su ke yi a yayin da mutumin ya ke nuna farin cikinsa game da shan kashi da Madrid ta yi.

Ga wasu daga cikin martanin mutane :

@elliotyemi ya ce: “Na yi wa Babanka alkawarin mallaka masa,rigar Barcelona da tikitin jirgin sama don kallon su suna wasa kai tsaye.”

@Depeculiar007 ya ce: “Ka gaya wa baban ka muna masa addua Allah ya ja kwana.

@AbjaFCB ya ce: “ai dole ya yi farin ciki yadda, Roma, Andield da Bayern suka yi Wannan abin ban dariya ne.”

@sirrdemilade ya ce: “Ka gaya wa popsy cewa fuskarsa da gidan sa zasu dawwama cikin farin ciki.”

Mace mai kamar maza: Ƙaramar yarinya ta lallasa abokin damben ta, ta samu gagarumar kyauta
Wata ƙaramar yarinyar ‘yar Najeriya ta nuna cewa idan aka zo fagen dambe to lallai ita ba kanwar lasa ba ce.

A wata wallafa a shafin Twitter da @Olaitan yayi, yarinyar ta lallasa wani yaro sa’ar ta yayin da su ka fafata dambe kamar ƙwararru. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Yarinyar ta yi dambe mai kyau
Yarinyar ta yi amfani da dogayen hannuwan ta akan yaron ta hanyar samun nasarar doke shi sosai. Ƙoƙarin sa wajen ƙare kansa daga dukanta bai wani tasiri ba.

A dai dai lokacin da bugun ta ke ƙoƙarun kai yaron ƙasa, sai alƙalin wasa ya nuna lokaci ya cika.
Yayin da ya ke mayar martani kan faɗan yarinyar mai ƙayatarwa, wani mutum mai amfani da @BikiniDoB a shafin Twitter, yayi alƙawarin ba yarinyar zunzurutun kuɗi har N50,000 domin ta sayi kayan dambe.
Labarun Hausa ta tattaro mu ku wasu daga ra’ayoyin mutane da su ka bayyana dangane da wasan damben na yaran guda biyu.

@DearPrechy ya ce:

“Waɗannan ƙananan yara ne. Dukkansu sun yi ƙoƙari. Eh nasan zaka ce mu taimaki wanda mu ke son taimako mu ma. Amma a irin wannan idan kana son nuna ƙauna, kowa da kowa ake ba. Hakan zai ƙara mu su ƙarfin guiwa. Da ace yarinyar ce ta sha kashi, mutane za su so su fifita ta. Ba adalci a duniya.

Waɗannan ƙananan yara ne. Dukkansu sun yi ƙoƙari. Eh nasan zaka ce mu taimaki wanda mu ke son taimako mu ma. Amma a irin wannan idan kana son nuna ƙauna, kowa yakamata ya samu. Hakan zai ƙara mu su ƙarfin guiwa. Da ace yarinyar ce ta sha kashi, mutane za su so su fifita ta. Ba adalci a duniya.

@Jeezy5Starr ya ce:

A raba musu kuɗin su biyu.

@OMTAworld ya ce:

Saboda yaron yasha kashi, shi ba za’a nuna masa ƙauna ba?

Mutumin ya mayar da martani:

Bai kamata in mayar mu ku martani ba amma zan yi. Ku na da damar da za ku iya taka rawar ku wajen taimakon yaron. Na zaɓi da in taimaki yarinyar. Ba abinda ya ba ku damar tambayar abinda na ga damar yi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe