22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Kano: Yadda kotu ta sakaya Ado a gidan yari akan satar dunkulen Maggi

LabaraiKano: Yadda kotu ta sakaya Ado a gidan yari akan satar dunkulen Maggi

Wata kotu da ke zama a Jihar Kano ta sakaya wani mutum mai shekaru 37 a gidan gyaran hali akan satar katan din dunkulen maggi, LIB ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Yusha’u Ado, mazaunin Goron Dutse Quarters ne da ke Kano, kuma yanzu haka ana zargin sa da cin amana tare da cuta.

Matar aure ta maka mijinta a kotu kan zargin yana cusa mata 'tissue' a gabanta
Kano: Yadda kotu ta sakaya Ado a gidan yari akan satar dunkulen Maggi

Tun farko, mai gabatar da kara, Sifeta Abdullahi Wada ya sanar da kotu yadda Jamilu Ibrahi na Galadanci Quarters ya kai korafi ofishin ‘yan sanda da ke Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Sifeta Wada ya ce ya yarda da Ado ta hanyar ajiye katan 260 na dunkulen maggi a shagon sa, bayan ya je kwashe magginsa ya ga katan 22 na maggi mai kimar N216,000 ya yi layar zana.

Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Alkalin, Dr Bello Khalid ya sakaya wanda ake zargin sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Afirilun 2022.

Gwada mazakuta ta nayi in gani ko tana aiki, Mai lalata yara maza ga kotu

Wani dan kasuwa a jihar Adamawa, Abubakar Barkindo, ya shiga hannun jami’an tsaro bayan an zarge shi da lalata yara maza biyu.

Daya daga cikin yaran shekararsa tara dayan kuma takwas kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Yayin da mahaifin yaran yake neman su ya ga yadda maniyyi ya ke zuba daga bakunan yaran guda biyu.

Kamar yadda yace:

“Na fita ne don neman yara na a kofar gida, sai aka shaida min cewa, Barkindo ya wuce da su gidan shi. Ban ji dadin hakan ba har sai da na furta hakan a gaban jama’a. Daga nan na duba sai naga maniyyi a bakunan yara na.”

Bayan gurfanar da mutumin da ake zargin a babbar kotun majistare ta daya a ranar Alhamis 17 ga watan Fabrairun 2022, ya amsa laifin sa, wanda ya saba wa sashi na 263 a dokar shari’ar jihar.

Yayin da ya fadi dalilin sa na yin lalata da yaran ta baki, cewa ya aikata hakan ne don ya fahimci ko mazakutar sa tana aiki. Ya ce ya fuskanci matsalar rashin mikewar al’aura.

A cewarsa ya yi amfani da magungunan gargajiya iri-iri don magance matsalar.

Bayan ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa, Alkali Abdullahi Digil ya bayar da umarnin sakaya shi a gidan gyaran hali sannan a dauki matakin da ya dace da laifin sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe