20.1 C
Abuja
Friday, December 9, 2022

‘Yan kudu sun hau fargaba akan ko dai Genevieve ta musulunta bayan ta yi wallafa da ayar Qur’ani, dadduma da kabari

Labarai‘Yan kudu sun hau fargaba akan ko dai Genevieve ta musulunta bayan ta yi wallafa da ayar Qur’ani, dadduma da kabari

Jarumar masana’antar fina-finan kudu, Genevieve Nnaji ta saki wani gajeren bidiyo a shafin ta na Instagram ya tayar da kura inda aka dinga musayar ra’ayi dangane da bidiyon, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Gajeren bidiyon ya nuna tunatarwa ne akan cewa duniyar nan ba komai bace ba a harshen turanci.

nnaji
‘Yan kudu sun hau fargaba akan ko dai Genevieve ta musulunta bayan ta yi wallafa da ayar Qur’ani, dadduma da kabari

A bidiyon an nuna cewa lahira ce tabbatacciya kuma komai na duniyar nan mafalki ne ba gaskiya ba.

Bidiyon ya nusar da mutane akan su farka, kuma an sanya ayar Al’Qur’ani mai girma da kuma dadduma.

Kamar yadda ake fadi a cikin bidiyon:

“Don Allah! Don Allah! Ku farka! Ku farka! Ku farka! Ko wanne mai rai mamaci ne.”

Bayan ta wallafa bidiyon nan, ya zama abin surutu da kuma fargaba, inda masoyanta musamman ‘yan kudu suka hau cece-kuce.

Sun yi fargaba akan kada fa ace jarumar nan ta musulunta ko kuma shirin musulunta take yi, idan ba haka ba, tana kirista, mai zai hada ta da wallafa ayar Qur’ani, dadduma ko kuma makabarta?

Duk da dai a bangaren story ta wallafa bidiyon kuma bayan awa daya story ke bata a Instagram. Amma sai wata ma’abociya instagram mai suna poshjournal ta kwafo kuma ta wallafa.

Kamar yadda ta wallafa:

“Mafarki ne kawai, Jaruma Genevieve Nnaji ta wallafa bidiyo da Qur’ani, dadduma da makabarta. Allah dai yasa jarumar kalau take.”

Nan da nan mabiyanta suka dinga cece-kuce, wasu suna fargabar kada fa ace musulunta ta yi, wasu kuma suna cewa ai a Najeriya kowa yana da damar yin addinin da ya ga dama. Akwai wadanda suke ganin wallafa ce ta tunatarwa ba wata manufa ba ta daban.

Wasu suna ganin cewa ko hakan ne, jarumar ta kauce hanya akan amfani da Qur’anin da ta yi.

Akwai wadanda suke ganin cewa dama biri ya yi kama da mutum don jarumar ta daina bin kowa a shafinta kuma ta sauya gabatarwar shafin nata.

Muna mata fatan tana da rabon shiga musulunci, Ameen.

Fitacciyar jarumar Nollywood Mo Bimpe ta Musulunta bayan ta auri Musulmi ta canja sunanta zuwa Rahmatullah

Wani rubutu da jarumi Adedimeji Lateef ya wallafa a shafin shi na kyakkyawar amaryar shi Mo Bimpe ya nuna cewa tuni jarumar ta canja sunanta zuwa na Musulmai.

A baya dai jarumar tana bin addinin Kiristanci sau da kafa, amma sakamakon auren jarumin da tayi wanda yake shi Musulmi ne ya sanya ta canja addini zuwa addinin Musulunci.

A rubutun da Adedimeji ya wallafa wanda ya yi alkawarin soyayyar shi gareta, ya bayyana cewa yanzu sunanta ya tashi daga Mo Bimpe ya koma Rahmatullah.

Jarumin ya ce:

“Alhamdulillah. Nagode wa Allah. Adebimpe Rahmatullah, ina so ki sani cewa ina sonki, kuma zan kasance a tare dake a koda yaushe. Ina miki barka da zuwa duniya ta.”


Masoyan su sunyi ta sanya musu albarka tare da fatan alkhairi a gare su kan wannan sabuwar rayuwa da za su fara a tare.

Kwanaki kadan bayan anyi bikin gargajiya a jihar Ekiti, Adedimeji Lateef da Mo Bimpe an daura musu aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar Laraba, 22 ga watan Disambar shekarar 2021.

A wani bidiyo da aka nuno ma’auratan a shafukan sadarwa, an nuno Adedimeji da Rahmatullah cikin fararen kaya sun rike juna cikin shauki na soyayya.

Bayan haka kuma an dauki jaruman hotuna da dama na aure a cikin dakin hotel da suka kama a lokacin bikin na su.

Haka kuma idan ba a manta ba a makon da ya gabata mun kawo muku labarin yadda fitacciyar jarumar Bollywood Sanam Chaudhry ta yi sallama da harkar fim.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe