24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wani ango mai shekaru 18 ya angwance da amaryar sa ‘yar shekara 16

LabaraiWani ango mai shekaru 18 ya angwance da amaryar sa 'yar shekara 16
Muhammad Ahmad Salihu 750x375 1
Ango mai shekaru 18 ya angwance da amaryar sa yar shekara 16

Al’ummar yankin sun cika da mamakin wannan aure

A ranar Juma’ar da ta gaba ta ne Tilden Fulani a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi ta yi ido biyu da wani abu mai ban mamaki da al’ajabi wanda ba a saba ganin irin sa ba,inda wani dan shekara 18 mai suna Muhammad Ahmad Salihu ya amarce da amaryarsa Sumayyah Adam Ibrahim mai shekaru 16 a duniya!

Taro ya gudana cikin farin ciki da jin dadi

Majiyar Daily Reality ta bayyana cewa, taron wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na kungiyar Ahlussunnah Wal Jama’a Izala na garin Tilden Fulani an gudanar da shi cikin lumana da shagali.
Yankin Arewacin kasa Najeriya yankine da yake cike da Fulani Mabiya addinin musulunci,wannan abu ne da aka saba. Aure shine cikar soyayya da ga zarar an kai ga fahimtar juna to aure shine abu nagaba saboda gujewa aikata alfasha kafin aure.

Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku, da salihai daga baga cikin ku. Idan sun kasance a cikin halin rashi, Allah zai wadãtar da su daga falalarSa, kuma Allah Yã kasance Mawadãci, Masani.” [Qur’an, 24:3]
Saboda haka muna taya Ango Muhammad Ahmad Salihu Murna da amaryar sa Asma’u,Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a dayyiba.

Zan dinga ba wa mijina Kashi 20 cikin 100 na Albashina domin ya kula da kansa, maza na shan wahala sosai- wata budurwa ta bayyana
Wata budurwa ‘yar Najeriya mai shafin Twitter @A_Blackwoman ta tayar da kura a shafinta na Twitter bayan ta bayyana irin kason da za ta bawa mijinta da ga cikin albashin ta. A cikin sakon da ta wallafa a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, budurwar ta ce hakika nauyi ya yi wa maza je yawa.

Zan ajiye kashi 30 domin amfanin gida

Budurwar ta kara da cewa tana son ba wa mijinta kashi 20 na albashin ta a matsayin hanyar tallafa masa, yayin da kashi 30 kuma za su shiga asusun amfanin gida.Ta ce ta na matukar tausayin mazan da ke aiki tukuru musamman masu aikin karfi, ta kara da cewa ta taba haduwa da wani makanike wanda yake kokarin neman na abinci, sai kuma wani mutum mai siyar da kayan lambu a tsakiyar rana.
Ga abinda ta ce:“…akwai wasu mutane da za ka gan su ,suna kokarin kwantar da hakarkarinsu za su dan huta su sami barci ko na minti daya zuwa biyu a saman siminti, a karkashin rana, mijina ya more,bazan bari ya sha wahala ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe