22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Da su bata kyautan Dubu Biyu gara su yi mata sanadin Dubu biyu:Bidiyon Yadda Iyayen wata budurwa ‘yar Najeriya Suka dauke ta Aikin Gini ya bayyana

LabaraiDa su bata kyautan Dubu Biyu gara su yi mata sanadin Dubu biyu:Bidiyon Yadda Iyayen wata budurwa 'yar Najeriya Suka dauke ta Aikin Gini ya bayyana
4d622edb9163b8f7 1
Bidiyon yadda iyayen wata budurwa suka dauketa aikin gini

Budurwa mai san’ar gini ta bayyana yadda iyayen ta suka jefa ta aikin leburanci

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta ba da shawarar yadda ta ji jiki bayan ta gama karatu.Budurwar mai suna Ekele Oyibo Patricia a shafin dandalin sada zumunta na Facebook ta bayyana cewa rayuwa bayan gama makaranta akwai kalubale sosai fiye da yadda ake tsammani.
Budurwar ta bayyana yadda iyayenta suka mayar da ita lebira saboda kawai ta nemi taimakon kudi a wurin su.
Na nemi a bani Naira 2000 saboda bukatar gaggawa amma iyayena suka ce sai dai su dauke ni aiki a matsayin lebira.”

Ta bayyana irin yadda aikin leburanci ke da wahala

Ta wallafa bidiyon ta a yayin da take aiki a wani wurin gini. A cikin ɗaya daga cikin bidiyon data wallafa,budurwar ta jinjina wa ’yan kwadago kuma ta yarda cewa duk da ya kasance aiki ne halartacce amma ba shi da sauƙi. A cikin hotunan da ta wallafa, har da wanda aka biyata dubu biyu kudin aikin ta cikin farin ciki.

Kadan daga cikin martanin mutane

Samuel Adejo: “Idan ki ka yi aikin dubu biyu zaki fi sanin darajar su…. hakan ya yi kyau.”
Terzungwe Inja ya ce: “yanzu a ce dalibar Najeriya ce haka, gbagba, aluta celeb…. “”Ya kamata a ce yanzu tana bautar kasa …. “Amma gwamnati ta,ki yin sulhu da malaman jami’a …”

Constance Palmer :”Gaskiya wannan ya ci a kirashi da gajeren labari hakan yayi kyaui! A haka za ku gina naku gidan nan ba da jimawa ba.”

Terseer Tarkumbur Odibo Nege: “Mu anan jos ya zama kamar Al’ada. “‘Yan mata sunayin aikin karfi a basu dubu biyu.”

Zan dinga ba wa mijina Kashi 20 cikin 100 na Albashina domin ya kula da kansa, maza na shan wahala sosai- wata budurwa ta bayyana


Wata budurwa ‘yar Najeriya mai shafin Twitter @A_Blackwoman ta tayar da kura a shafinta na Twitter bayan ta bayyana irin kason da za ta bawa mijinta da ga cikin albashin ta. A cikin sakon da ta wallafa a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, budurwar ta ce hakika nauyi ya yi wa maza je yawa.

Zan ajiye kashi 30 domin amfanin gida

Budurwar ta kara da cewa tana son ba wa mijinta kashi 20 na albashin ta a matsayin hanyar tallafa masa, yayin da kashi 30 kuma za su shiga asusun amfanin gida.Ta ce ta na matukar tausayin mazan da ke aiki tukuru musamman masu aikin karfi, ta kara da cewa ta taba haduwa da wani makanike wanda yake kokarin neman na abinci, sai kuma wani mutum mai siyar da kayan lambu a tsakiyar rana.
Ga abinda ta ce:

“…akwai wasu mutane da za ka gan su ,suna kokarin kwantar da hakarkarinsu za su dan huta su sami barci ko na minti daya zuwa biyu a saman siminti, a karkashin rana, mijina ya more,bazan bari ya sha wahala ba.“

Kadan daga cikin martanin mutane:

@tegaudi ya ce: “ki bani dama in gabatar da kaina a gareki kafin kuraye su rigani yin wuff da ke…. dan Allah nawa ne zai samar da kashi 20?. In aka maidashi dala.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe