24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Da duminsa: Diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan ta haifi da namiji

LabaraiDa duminsa: Diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan ta haifi da namiji

Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan ta haifi yaro namiji a kasar Turkiyya. Wata majiya ta kusa da ‘yan uwan Hanan ta sanar da Solacebase cewa ta haihu na a ranar Lahadi.

Solacebase ta ruwaito yadda Muhammad Turad ya auri Hanan, diyar shugaban kasa ta yi aure a watan Satumban 2020.

This image has an empty alt attribute; its file name is Hanan-Haihu-509x384.jpg
Da duminsa: Diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan ta haifi da namiji

An samu bayanai akan cewa yanzu haka daga jaririn har mahaifiyar sa suke cikin koshin lafiya. Shafin arewa family weddings na Instagram ma ya tabbatar da batun haihuwar ta.

Shifin ya ruwaito cewa sun sa wa jaririn suna Muhammad Zayd. Allah ya raya.

An tsaurara tsaro a Kano yayin da ake shirin daurin auren dan gidan Shugaban Kasa da diyar Sarkin Bichi

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci daurin auren dansa Yusuf wanda za a daura da diyar Sarkin Bich, a jihar Kano gobe, shugaban kwamitin kula da harkokin bikin, Shehu Ahmed shine ya sanar da haka ga manema labarai jiya.

Ahmed ya ce ana sa ran manyan masu fada a ji dake rike da manyan madafun iko na gida Najeriya dana kasashen ketare za su halarci wajen daurin auren, wanda za a daura da misalin karfe 1:30 na rana bayan an kammala sallar Juma’a.

An gano cewa a daren jiya gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da ma’aikatan ofishin ga surukin shugaban kasar, Sarkin Bichi, Mai Martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Ahmed ya ce:

Muna da manyan abubuwa guda biyu ranar Juma’a da Asabar a Bichi – daurin auren dan gidan Buhari da diyar Sarkin Bichi da kuma nadin sarauta da Sarkin zai yi.

Ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai halarci wajen daurin auren dan na shi da diyar Sarkin Bichi a garin Bichi ranar Juma’a.

Za a gabatar da addu’o’i na musamman a babbban Masallacin Bichi daa misalin karfe 4:30 na yamma.

Dangane da bikin nadin sarauta kuwa da Sarkin zai yi, za a gabatar da lacca kan nadin sarauta a kwalejin ilimi ta tarayya dake Bichi a ranarr Alhamis (yau); yayin da za a gudanar da bikin gabatar da ma’aiikatan ofis a filin wasa na Bichi ranar Asabar.

Hakanan kananan kwamitoci sun gama shirye-shirye don tabbatar da cewa an gudanar da wadannan muhimman abubuwa guda biyu.

An samu tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano, musamman ma a garin Bichi, gabannin daurin auren da za a yi a gobe da kuma nadin sarauta ranar Asabar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: The Nation

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe