24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Neja: Yadda fusatattun matasa suka fattataki dan majalisar yankin su daga zuwa ta’aziyya

LabaraiNeja: Yadda fusatattun matasa suka fattataki dan majalisar yankin su daga zuwa ta’aziyya

Mutanen mazabar Magama sun kai farmaki, gami da fatattakar dan majalisar da ke wakiltar yankin su a Jihar Neja, Suleiman Musa Nasko, LIB ta ruwaito.

An kai wa Nasko hari a ranar Asabar, 19 ga watan Maris, yayin da ya je ta’aziyya ga iyalan wadanda yan bindiga suka halaka, inda DPO da jami’an tsoro guda shida suka rasa rayukansu.

Neja: Yadda fusatattun matasa suka fattataki dan majalisar yankin su daga zuwa ta’aziyya
Neja: Yadda fusatattun matasa suka fattataki dan majalisar yankin su daga zuwa ta’aziyya

Fusattatun matasan mazabar, wadanda yawancin su matasa ne, sun masa eho, gami da jifan jerin motocin da suka rako shi har wajen garin, yayin da su ke cewa “Ba ma yi”.

Majiyoyi sun labarta wa Daily Trust yadda dan majalisar ya yi nasarar haduwa da hakimin Auna

Ya yin da wasu matasan da su ka yi gungu suka fara daga murya suna cewa “kalma daya tak”, hakan ya yi sanadiyyar rikici tsakanin masoyan sa da fusattatun matasan.

Dan majalisar ya yi kokarin tserewa ba tare da ya samu rauni ba, saboda jami’an tsaron da yake tare dasu.

Kakakin dan majalisar, Sahabi Mahmud, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana yadda Nasko bai yi farin cikin aukuwar lamarin ba.

“Wata hayaniya ce tsakanin magoya bayan dan majalisar da ke wakiltar Magama, Hon. Suleiman Musa da wasu matasa,” a cewar Mahmud.

“Da gaske lamarin ya auku a Auna, inda dan majalisar ya je ta’aziyya ga iyalin daya daga cikin ‘yan sakan da aka halaka tare da sauran jami’an tsaro a Nasko.

“Sai dai, a lokacin da mu ke kan hanyar fita daga yankin ne, wasu matasa suka fara ihu suna cewa ‘,ba ma yi’ wanda ya yi sanadiyyar barkewar rikici tsakanin magoya bayan dan majalisar.”

Amma, ko bayan ya samu labarin yadda mutanen shi su ka yi fada da juna, bai yi farin cikin hakan ba.”

Fusatattun matasa sun kone makarantar Abdulmalik wanda ya kashe Hanifa a Kano

Matasa sun sanyawa makarantar Noble Kids Comprehensive College wuta, wacce ke kan hanyar Warshu Hospital Road, Kawaji Kano, sakamakon kisan Hanifa Abubakar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban makaratar, Abdulmalik Tanko, ya yi garkuwa tare da kuma kashe Hanifa bayan ya karbi kudin fansa daga hannun su iyayenta.

An kone makarantar su Hanifa da daddare

Lamarin ya faru da tsakar daren ranar Lahadi 23 ga watan Janairu, 2022, inda a yayin da jaridar Daily Nigerian ke daukar wannan rahoto, wutar na cigaba da ci a makarantar ganga-ganga.

Tuni dai dama gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin kulle makarantar, bayan kama shugaban makarantar Abdulmalik Tanko da kisan Hanifa mai shekaru biyar a duniya.

Akwai maganganu da ake ta yadawa dangane da kisan, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin tabbatar da adalci ga duka wadanda ke hannu a wannan ta’addanci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe