24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Bidiyon matashi cikin katuwar mota yana zolayar tsohon hedimastan su da ke kan babur ya janyo surutai

LabaraiBidiyon matashi cikin katuwar mota yana zolayar tsohon hedimastan su da ke kan babur ya janyo surutai

Wani matashi yabi tsohon hedimastan makarantar su, inda yayi amfani da damar wurin zolayar shi, matakin da ya dauka ya tada tarzoma a kafafan sada zumuntar zamani, LIB ta ruwaito.

A guntun bidiyon da @gossipmilltv suka wallafa a Instagram ya fara da nuna yadda wani mutum dan Najeriya da ya tuko mota ta bayan wani dan acaba da ke dauke da fasinja namiji.

dalibi 1
Bidiyon matashi cikin katuwar mota yana zolayar tsohon hedimastan su da ke kan babur ya janyo surutai

Ya yi hanzarin tukin don riskar dan acabar, gami da tabbatar da cewa tsohon hedimastan makarantar su ne ya gani.

An ji yadda matashin yake zolayar fasinjan, inda ya fadi a harshen Yarabanci, cewa tsohon hedimastan shi ne malamin da ya ce musu a baya, ba za su yi arziki ba tare da sun yi karatu ba.

Ya cigaba da kwalawa fasinjan dan acaban da sunan da ake mishi lakabi dashi.

Tsohon hedimastan ya yi kamar bai ji kiran matashin ba gaba daya, sannan ya juyar da fuskar sa ta dayan bangaren, kamar zai boye fuskarsa.

Hakan ya zanyo cecekuce karkashin wallafar bidiyon.

@__good_bhad__boi ya ce:

” Shugaba ya koya min karatu a makaranta… Shugaba bai samu aiki mai kyau ba.

“Shugaba ya ganni a mota ta, amma ya yi kamar bai ganni ba.

“Shugaba ka kalle ni da kyau ni ne dalibin ka, kada ka ji kunya.”

@thonia_onopiri ya ce:

“Wannan ba abun dariya ba ne gaba daya, malamai, dokoki, karatuttukan, duk mutanen nan su ne suka bamu ilimi ta wannan hanyar ko wata hanyar a shekarun da su ka shude, saboda haka sun cancanci girmamawa daga garemu.

“Duk irin yadda suka takura mana, burin su kawai su tabbatar mun zama mutanen kwarai ga al’umma wata rana.”

@ralph_newrevelation ya ce:

“Matasan zamanin nan basu da kima. Wa ya horar da su, waya raine su?… bayyanan nan abun kunya, ba ‘da’a, ba kauna. Kash!!

@talk_anyhow_you_collect yayi tsokaci:

“Kaddarar kowa daban ce, a kalla dai yana samun kudin halas ba satar wa mutane kudi yake ba.”

Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

A wani bidiyon TikTok wanda shafin LIB suka wallafa an ga budurwar cike da kunci har tana bayyana cewa shekarun su 6 tare da saurayin.

Ta ce yanzu haka ya yi danwaken zagaye zai aure wata budurwar ta daban wacce mahaifiyar sa ta zaba masa.

Ta ce shekarun su 6 suna soyayya cike da shauki amma duk da haka ya share ta zai sauya akalar soyayyar sa inda ya koma wurin wata daban.

Yanzu haka ta shiga damuwa saboda halin da ta tsinci kan ta duk da soyayyar da suka dade suna yi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe