24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

In har Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, zan bar Najeriya, Jagoran PDP, Bode George

LabaraiIn har Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, zan bar Najeriya, Jagoran PDP, Bode George

Jagoran jam’iyyar PDP, kuma tsohon shugaban hukumar kula da madatsun ruwa, Bode George ya ce zaiyi wa Najeriya kaura idan Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya, LIB ta ruwaito.

Yayin tattaunawa da manema labarai a Legas ranar Asabar 19 ga watan Maris, George ya ce, Tinubu zai tabbatar da iyalinsa sun mamaye mukamai masu gwabi idan ya zama shugaban kasa, inda ya kara da cewa tsohon gwamnan bai tabuka aikin da ya taka kara ya karya ba da har ya cancanci kujerar.

pdp cheiftain
In har Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, zan bar Najeriya, Jagoran PDP, Bode George

Cewarsa;

“Ina farin ciki da rattaba hannun da shugaban kasa yayi akan sabuwar dokar zabe. Idan har ko ta yaya ne ya shiga fadar shugaban kasa (yana nufin Tinubu), bazan ci gaba da zama a kasar nan ba.

“Kuma ba da wasa nake ba. Zan iya tafiya Ghana, in yi zama na a can, in zuro muku na mujiya daga nesa. Zaku ga abunda zai faru.

“Wannan mai juya jihar Legas din zai samo wasu masu yankar aljihu daga wani wurin da zasu yi awon gaba da kudaden ku. Matar sa zata zama shugaban majalisar dattawa. Dan shi kuma zai zama gwamnan Legas. Ita kuma ‘yar sa zata zama sarauniyar Najeriya.

“Me yayi don tabbatar da ya cancanci wani ya girmamashi a kasar nan?

“Babu abunda yayi. Hakikanin gaskiya, diyar ‘yar uwata ta kira mi. Ta ce ‘wasu mutanensu na yamadidi cewa yana bani ‘yan kudade. Wai Bola yana bani kudi’.

“Ya kawo kudin ya gani. Zan ce mai ya biyoni Lagos Island – mutane na cikin yunwa a can. A can na taso – a Lagos Island.”

Ana kulla kullalliyar hana Atiku, Saraki da Tambuwal fitowa takara a jam’iyyar PDP

Sarkakiya ta balle a jam’iyyar PDP yayin taron jiga-jiga wanda aka yi a daren Litinin, hakan ya sa shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorcha Ayu ya yi gaggawar dakatar da taron zuwa yau, The Nation ta ruwaito.

Hayaniyar ta samo asali ne bayan wasu shugabanni daga kudu suka fara batun cewa a cire mambobin da suka koma APC a baya sannan suka kara dawowa PDP daga cikin jerin wadanda zasu tsaya takarar shugaban kasa.

Wani gwamnan kudu kamar yadda majiyoyi suka bayyana ya amince da wannan batu.

Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da kuma gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal suna daga cikin sanannun mutanen da suka bar jam’iyyar PDP zuwa APC don su tsaya takara a zaben 2015.

Sai dai sun kara komawa PDP bayan sun kasa zama inuwa daya da fadawan Muhammadu Buhari da kuma shugabannin APC.

Wasu daga cikin su sun ci zabe yayin da wasu suka fadi a zaben 2019 karkashin jam’iyyar PDP.

Duk suna harin tsayawa takarar shugaban kasa.

Wadanda suka kawo batun cire masu sauya shekarar sun tsaya akan cewa komawar su APC ne ya janyo jam’iyyar PDP ta fadi zabe a 2015.

Sun ce PDP ta shiga mawuyacin hali ne saboda abinda wadannan mutane suka yi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe