29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Mace mai kamar maza: Ƙaramar yarinya ta lallasa abokin damben ta, ta samu gagarumar kyauta

LabaraiMace mai kamar maza: Ƙaramar yarinya ta lallasa abokin damben ta, ta samu gagarumar kyauta

Wata ƙaramar yarinyar ‘yar Najeriya ta nuna cewa idan aka zo fagen dambe to lallai ita ba kanwar lasa ba ce.

A wata wallafa a shafin Twitter da @_Olaitan_ yayi, yarinyar ta lallasa wani yaro sa’ar ta yayin da su ka fafata dambe kamar ƙwararru. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Yarinyar ta yi dambe mai kyau

Yarinyar ta yi amfani da dogayen hannuwan ta akan yaron ta hanyar samun nasarar doke shi sosai. Ƙoƙarin sa wajen ƙare kansa daga dukanta bai wani tasiri ba.

A dai dai lokacin da bugun ta ke ƙoƙarun kai yaron ƙasa, sai alƙalin wasa ya nuna lokaci ya cika.

Wani bidiyo ya nuna lokacin da yaron ya samu da ƙyar ya riƙe igiyoyin filin bayan yasha wani bugu mai girma a hannun ta. An fafata sosai a wasan.

Yarinyar ta samu kyautar N50,000

Yayin da ya ke mayar martani kan faɗan yarinyar mai ƙayatarwa, wani mutum mai amfani da @BikiniDoB a shafin Twitter, yayi alƙawarin ba yarinyar zunzurutun kuɗi har  N50,000 domin ta sayi kayan dambe.

Ga wallafar da mutumin yayi anan ƙasa:

Ga sauran bidiyoyin nan a ƙasa:

Mutane sun bayyana ra’ayoyin su

Labarun Hausa ta tattaro mu ku wasu daga ra’ayoyin mutane da su ka bayyana dangane da wasan damben na yaran guda biyu.

@DearPrechy ya ce:

“Waɗannan ƙananan yara ne. Dukkansu sun yi ƙoƙari. Eh nasan zaka ce mu taimaki wanda mu ke son taimako mu ma. Amma a irin wannan idan kana son nuna ƙauna, kowa da kowa ake ba. Hakan zai ƙara mu su ƙarfin guiwa. Da ace yarinyar ce ta sha kashi, mutane za su so su fifita ta. Ba adalci a duniya.

Waɗannan ƙananan yara ne. Dukkansu sun yi ƙoƙari. Eh nasan zaka ce mu taimaki wanda mu ke son taimako mu ma. Amma a irin wannan idan kana son nuna ƙauna, kowa yakamata ya samu. Hakan zai ƙara mu su ƙarfin guiwa. Da ace yarinyar ce ta sha kashi, mutane za su so su fifita ta. Ba adalci a duniya.

@Jeezy5Starr ya ce:

A raba musu kuɗin su biyu.

@OMTAworld ya ce:

Saboda yaron yasha kashi, shi ba za’a nuna masa ƙauna ba?

Mutumin ya mayar da martani:

Bai kamata in mayar mu ku martani ba amma zan yi. Ku na da damar da za ku iya taka rawar ku wajen taimakon yaron. Na zaɓi da in taimaki yarinyar. Ba abinda ya ba ku damar tambayar abinda na ga damar yi.

Yaron da ya kwaikwayi gadar Kano da wasa ya samu gurbin karatu a kasar Amurka, an kuma yiwa mahaifiyarshi kyautar miliyan daya

Wani ƙaramin yaro ya zama sanadiyyar samun tagomashin iyayen sa bayan da wani kamfanin gine-gine ya lura da aikin sa.

Ƙaramin yaron ɗan Najeriya mai suna Musa Sani ya zama abin magana akan yanar gizo bayan yayi irin ɗaya daga cikin gadojin sama na Kano wanda ya gina da abubuwan da ya samo daga nan cikin gida Najeriya. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Da yake wallafa hotunan Musa tare da ƙirƙirarsa a shafin Twitter, wani ɗan Najeriya mai suna @OvieNews ya bayyana cewa wani kamfanin gine-gine mai suna Ronchess Global Resources, ya ba Musa gurbin karatu a jami’a a ƙasar Amurka kyauta.

@OvieNews wanda ya bayyana cewa shugaban kamfanin ya tuntuɓe sa, inda ya ƙara da cewa kamfanin ya ba mahaifiyar Musa naira miliyan ɗaya (N1m) ta fara sana’a, yayin da kuma aka ba mahaifin shi aiki a kamfanin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe