27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

‘Yan sanda sun cafke wata mata wacce ta ƙona ɗuwawun ɗiyar mijinta da wuƙa mai zafi

Labarai'Yan sanda sun cafke wata mata wacce ta ƙona ɗuwawun ɗiyar mijinta da wuƙa mai zafi

‘Yan sandan jihar Bayelsa sun cafke wata mata mai suna Esther Otoniye, bisa laifin ƙona ɗuwawun ɗiyar mijin ta mai shekaru 10 da wuƙa mai zafi.

Otinoye wacce aka cafke a gidan su da ke Akenfa wajen birnin Yenagoa, babban birnin jihar, ta bayyana cewa ƙaramar yarinyar ta sharara mata ƙarya ne. Jaridar Independent.ng ta rahoto.

'Yan sanda
‘Yan sanda sun cafke wata mata wacce ta ƙona ɗuwawun ɗiyar mijinta da wuƙa mai zafi. Hoto daga Independent.ng

Jikin ƙaramar yarinyar yasha tabbai sosai waɗanda aka zargin ta same su ne ta hanyar shan bugu sosai.

‘Yan sanda sun ɗamƙe matar

An samo cewa a ranar Asabar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ben Okolo, ya bayar da umurnin cafke Otinoye bayan wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin mata da ƙananun yara sun shigar da ƙorafe-ƙorafe a kan ta.

Sai dai ta musanta ƙona ɗuwawun yarinyar da wuƙa mai zafi, inda ta bayyana cewa ruwan zafi ne ya zubo mata a ɗuwawun bisa tsautsayi.

Amma, yarinyar ta amsa cewa ta sharara wa matar ƙarya inda ta hukunta ta hanyar ƙona mata ɗuwawu da wuƙa mai zafi.

Ɓangaren kula da jinsi na hukumar ‘yan sandan jihar ma su lura da lamarin sun miƙa yarinyar asibitin ‘yan sanda domin duba lafiyar ta.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da cafke Esther Otinoye bisa tuhumar aikata laifin, inda ya bayyana cewa an miƙa lamarin zuwa ga hannun ‘State Criminal Investigation and Intelligence Department’ (SCIID).

Ya bayyana cewa:

Laifi ne wanda matar aure ta yi amfani da wuƙa mai zafi ta yi raunika ga yarinyar mijinta mai shekaru 10 a duniya. Ana cigaba da gudanar da bincike.

‘Yan sanda sun kama magidanci da ya kashe kaninsa bayan ya kama shi yana lalata da matar sa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Niger, ta kama wani magidanci mai suna Tambaya Usman, saboda ya kashe dan yayan baban sa, Umar Musa, sakamakon kama shi yana lalata da matarsa. 
Lamarin ya faru ne a farkon wannan watan a kauyen Jaguwa a  karamar hukumar Rafi dake jihar Niger . 

‘Yan sandan dake yankin Kagara, sune suka kama wanda ake zargin. Mai laifin ya bayyana cewa, ya daddatsa wa wanda aka kashe din adda ne a kansa, sakamakon dadewa da yayi yana lalata da matarsa a baya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe