22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

MashaAllah: Jaruma Saima Muhammad ta yi aure

LabaraiKannywoodMashaAllah: Jaruma Saima Muhammad ta yi aure

Tsohuwar jaruma wacce ta yi shuhura a masana’antar Kannywood, Saima Muhammad ta yi auren ta cikin rufin asiri.

Kamar yadda Rashida Mai Sa’a ta shaida a shafinta na Instagram inda ta sanya hoton ta tana yi mata fatan alheri.

amarya saima
MashaAllah: Jaruma Saima Muhammad ta yi aure

Sai dai jarumar bata bayyana wanene mijin ko kuma inda yake ba. Hoton ta kadai ta wallafa tana yi mata fatan alheri.

Dama tun kwanaki jarumar a wata hira da BBC Hausa ta yi da ita tace ta kosa ta yi aure, sai ga shi Allah ya cika mata burin ta.

A karkashin wallafar Rashida, ta bayyana cewa:

“Alhamdulillah, Allah ya sa alkhairi. Aunty Salma ta amarce shekaran jiya da angon ta.

“Allah ya ba da zaman lafiya uwa ta, Allah ya kawo ‘yan biyu kuma Allah ya nuna mana na ‘yan baya.”

Nan da nan mutane suka fara tsokaci karkashin wallafar suna yi mata fatan alkhairi.

Muna mata fatan samun zaman lafiya da sabon abokin rayuwar ta da zuri’a dayyiba. Ameen.

Bayan watanni 7, auren sirrin da Zarah Diamond ta yi ya mutu

Tashar Tsakar Gida ta bayyana yadda suka samu labari akan mutuwar auren da Zara Diamond ta yi a sirri a watanni 6 zuwa 7 da suka gabata.

Kenan ta bi sahun su Rahama Hassan, Hafsat Shehu da su Mansura Isah.

Tsawon lokaci kenan da Zara Diamond ta bude shafukan sada zumunta na Instagram da TikTok inda take wallafe-wallafen ta cike da nishadi.

A kwanakin nan ne abubuwa suka sauya salo don a lokacin da ta yi auren sirri ta goge duk wasu shafukanta na kafafen sada zumunta kuma ta bukaci shafukan masoyanta wato Fan Page da su goge don ta yi aure.

Tun bayan auren ta, ba a fiye ganin jarumar ba sai a kwanakin nan da abubuwa suka sauya inda ake ganin tana bidiyo da kananun kaya kuma babu dankwali akanta.

Wannan sauyin yasa mutane suka fara sanya alamun tambaya domin lamarin da mamaki, don ko hoto ta daina wallafawa ballantana batun bidiyo.

Wata majiya ta tabbatar wa Tashar Tsakar Gida cewa tabbas aurenta ya dan jima da mutuwa sai dai bata riga ta bayyana bane.

Hakan yasa Tashar Tsakar Gida ta tuntubi wani furodusa da ke da alaka da ita, Sunusi Multimedia don ya bayar da lambar wayanta a ji daga bakin ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe