24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Zann dinga ba wa mijina Kashi 20 cikin 100 na Albashina domin ya kula da kansa, maza na shan wahala sosai- wata budurwa ta bayyana

LabaraiZann dinga ba wa mijina Kashi 20 cikin 100 na Albashina domin ya kula da kansa, maza na shan wahala sosai- wata budurwa ta bayyana
2d4f00420c78e634
wata budurwa ta bayyana cewa dolene mijinta ya amfana da kaso 20 cikin 100 na albashinta

In da so da kyautatawa wata budurwa tace dole mijinta ya ci gajiyar arzikinta

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai shafin Twitter @A_Blackwoman ta tayar da kura a shafinta na Twitter bayan ta bayyana irin kason da za ta bawa mijinta da ga cikin albashin ta. A cikin sakon da ta wallafa a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, budurwar ta ce hakika nauyi ya yi wa maza je yawa.

Zan ajiye kashi 30 domin amfanin gida

Budurwar ta kara da cewa tana son ba wa mijinta kashi 20 na albashin ta a matsayin hanyar tallafa masa, yayin da kashi 30 kuma za su shiga asusun amfanin gida.Ta ce ta na matukar tausayin mazan da ke aiki tukuru musamman masu aikin karfi, ta kara da cewa ta taba haduwa da wani makanike wanda yake kokarin neman na abinci, sai kuma wani mutum mai siyar da kayan lambu a tsakiyar rana.
Ga abinda ta ce:

“…akwai wasu mutane da za ka gan su ,suna kokarin kwantar da hakarkarinsu za su dan huta su sami barci ko na minti daya zuwa biyu a saman siminti, a karkashin rana, mijina ya more,bazan bari ya sha wahala ba.

Kadan daga cikin martanin mutane:

@tegaudi ya ce: “ki bani dama in gabatar da kaina a gareki kafin kuraye su rigani yin wuff da ke…. dan Allah nawa ne zai samar da kashi 20?. In aka maidashi dala.”

@Batundepictures ya ce: “bari na dauki hoto na nuna wa budurwa ta saboda nima ta fara bani kashi 20 cikin albashinta.”

@austine_okpegwa ya ce: “Allah ya albarkaci kyakyawar zuciyar ki.Kuma ina miki fatan samun miji nagari”

Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

Wata budurwa ta shiga cikin matsanancin tashin hankali kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo tana rusa kuka.

A wani bidiyon TikTok wanda shafin LIB suka wallafa an ga budurwar cike da kunci har tana bayyana cewa shekarun su 6 tare da saurayin.
Ta ce yanzu haka ya yi danwaken zagaye zai aure wata budurwar ta daban wacce mahaifiyar sa ta zaba masa.

Ta ce shekarun su 6 suna soyayya cike da shauki amma duk da haka ya share ta zai sauya akalar soyayyar sa inda ya koma wurin wata daban.
Yanzu haka ta shiga damuwa saboda halin da ta tsinci kan ta duk da soyayyar da suka dade suna yi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe