29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

‘Yan bindigan IPOB sun ƙone ofishin ‘yan sanda, sun halaka jami’ai 2 a jihar Imo

Labarai'Yan bindigan IPOB sun ƙone ofishin 'yan sanda, sun halaka jami'ai 2 a jihar Imo

‘Yan sanda mutum 2 sun rasa rayukan su lokacin da ‘yan bindiga su ka cinnawa ofishin ‘yan sanda na Umuguma a ƙaramar hukumar Owerri ta yamma da safiyar yau Asabar a jihar Imo.

Harin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan mataimakin sifeton ‘yan sanda (AIG), mai kula da shiyya ta 9, Umuahia, Isaac Akinmoyede, ya bar jihar bayan ziyarar kwana ɗaya da ya kai.

Haka kuma lamarin na zuwa ne bayan wasu jami’ai waɗanda su ke cikin wata tawagar haɗin guiwa ta tsaro sun rasa rayukan su bayan da ‘yan bindiga su ka farmaki motar sintirin su a garin Okigwe.

Yadda lamarin ya auku

Daily Trust ta samo cewa ‘yan bindigan bayan isar su sun kulle dukkanin hanyoyin zuwa ofishin ‘yan sandan, ciki kuwa harda wacce ta ke zuwa hedikwatar ƙaramar hukumar.

Bayan nan sai su ka farmaki ofishin ‘yan sandan inda su ka dinga jefa abubuwa masu fashewa a cikin ginin.

An kuma ƙara samun cewa bayan sun cinnawa ofishin wuta, sun jira domin kai wa jami’an da ke neman tsira farmaki daga wutar.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa ‘yan sanda biyu sun sha ruwan harsashai. An bayyana sunayen su a matsayin Ifeanyi da Iyke. Waɗanda kuma ɗalibai ne a jami’ar jihar Imo da ke a Owerri.

Hukumar ‘yan sanda ba ta ce komai ba

Ba a samu jin ta bakin Michael Abattam, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ba dangane da lamarin.

Ku taimaka ka da ku tafi yajin aiki, AIG ya roƙi ‘yan sanda

Mataimakin babban sifeton ‘yan sanda (AIG) na shiyya ta 9, Isaac Akinmoyede, ya roƙi ‘yan sandan Najeriya da kada su tsunduma yajin aiki bisa rashin samun ababen jindaɗi a wurin aikin su.

Akinmoyede, wanda yayi wannan roƙon yayin wata ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai babban ofishin ‘yan sandan jihar Imo jiya Juma’a, ya bayyana cewa ba dalilin yin yajin aikin saboda bai da wani amfani. Jaridar The Guardian ta rahoto.

Ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma babban sifeton ‘yan sanda na ƙasa (IGP), Usman Baba, sun sanya matakai domin ƙara samun jindaɗin jami’an, inda ya roƙe su da su ƙara haƙuri domin cin moriyar shirin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe