22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Ku taimaka ka da ku tafi yajin aiki, AIG ya roƙi ‘yan sanda

LabaraiKu taimaka ka da ku tafi yajin aiki, AIG ya roƙi 'yan sanda

Mataimakin babban sifeton ‘yan sanda (AIG) na shiyya ta 9, Isaac Akinmoyede, ya roƙi ‘yan sandan Najeriya da kada su tsunduma yajin aiki bisa rashin samun ababen jindaɗi a wurin aikin su.

Akinmoyede, wanda yayi wannan roƙon yayin wata ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai babban ofishin ‘yan sandan jihar Imo jiya Juma’a, ya bayyana cewa ba dalilin yin yajin aikin saboda bai da wani amfani. Jaridar The Guardian ta rahoto.

Gwamnati na ƙoƙari wajen jindaɗin ‘yan sanda

Ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma babban sifeton ‘yan sanda na ƙasa (IGP), Usman Baba, sun sanya matakai domin ƙara samun jindaɗin jami’an, inda ya roƙe su da su ƙara haƙuri domin cin moriyar shirin.

A cewar sa, biyan ƙarin kaso 20 na albashin jami’an na nan tafe nan ba da jimawa ba.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin jami’an wajen jajircewar su wajen tabbatar da doka da oda inda ya ƙara da cewa shiyyar a ƙarƙashin jagorancin sa zai cigaba da ba su cikakkiyar kulawa.

Ya roƙe su da kada su shiga yajin aiki

Akinmoyede ya ce:

Mun saurari rahotannin da ke hasashen cewa ‘yan sanda za su tafi yajin aiki. Sai dai hakan bai da amfani kuma ba dalilin yin sa.

Saboda haka ina roƙon ku da kada ku yi tunanin yajin aiki, saboda shugaban ƙasa da IGP su na iyakar bakin ƙoƙarin su wajen cigaba da samar da walwala ga jami’an ‘yan sanda.

Ina da tabbacin cewa jami’an ‘yan sandan wannan jiha da wannan shiyyar gabaɗaya na da jajircewa wajen gudanar da aikin su. Na yaba sosai wajen ƙoƙarin ku na rage laifuka a jihar mu”

Tun farko da ya ke jawabin sa, kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Imo, CP Rabiu Hussaini, ya bayar da tabbacin cewa jami’an sa ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen kawo karshen laifuka a jihar Imo.

Neja: Wani jami’in ‘yan sanda ya rasu bayan sun halaka ‘yan bindiga da dama yayin harin da suka kai wani gini

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani ɗan sanda guda a jihar Neja yayin wani hari da suka kai ofishin ‘yan sanda reshen Bangi a karamar hukumar Mariga, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, Premium Times ta ruwaito.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Abubakar Bello, Mary Noel-Berje ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a ranar Laraba

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe