27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Sojoji sun bude wa mata ta wuta bayan sun nemi ta yi tsirara ta ki, Sheikh Ibrahim Zakzaky

LabaraiSojoji sun bude wa mata ta wuta bayan sun nemi ta yi tsirara ta ki, Sheikh Ibrahim Zakzaky

Sheikh Ibrahim Zakzaky shugaban mabiya shi’a na Najeriya gaba daya ya bayar da cikakken labarin artabun su da sojoji.

A wata hira da BBC Hausa ta yi da shi, ya shaida yadda sojoji suka halaka daruruwan mutane kafin su isa dakin da yake zaune da matar sa da yaransa na cikinsa 4.

zakzaky
Sojoji sun bude wa mata ta wuta bayan sun nemi ta yi tsirara ta ki, Sheikh Ibrahim Zakzaky

Kamar yadda ya bayar da labarin, bai san irin yawan harsasan da sojoji suka harba masa a cinyar sa ba, don sai da ta ka ga dagargajewa.

Ya kara da bayyana yadda sojojin suka nemi matarsa ta yi tsirara amma ta ki amincewa, hakan ya hassala su suka bude musu wuta.

A cewarsa:

“Sun kama maza, mata da yara. Daga baya suka saki yara da mata, sai da ta kai ga saura maza 163 wadanda suka wuce Kaduna da su.

“Daga nan suka tasa keya ta da mata ta suka nufi Abuja da mu. Sun kai mu da farko asibitin sojoji, sannan na SSS. Mun kai wata 3 a asibiti, daga Disamba zuwa March. Domin sun ragargaza min cinya ta dama da harsashi.”

Zakzaky ya ce mutane 4 ne suka tsugunna cikin falon sa suna ruwan harsasai.

Ya ci gaba da cewa:

“Suna zuwa suka ce wa matata, ta cire kayan ta. Tana cewa ba za ta cire ba sai suka ce ‘fire’, suka bude mana wuta. Sai da dakin ya turnuke da harsashin. Sai dai kauri kawai kake ji.”

Ya ce take a wurin suka harbi yaron sa dan shekara 13 a goshi wanda ya fadi ya mutu take yanke.

Akwai yaran sa na cikin sa, maza 3 da mace daya da suka halaka a wurin a cewarsa. Sannan akwai yaran riko da ‘ya’yan ‘yan uwansa masu zama a gidan wadanda duk aka harbe su.

El-Zakzaky: Za mu maka gwamnatin Kaduna gaban kotu – Lauya

A jiya ne dai wata babbar kotu a jihar Kaduna ta wanke ta kuma sallami shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmai, wato Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat.

Bayan zaman awa takwas da aka shafe a kotun, Alkalin Kotun Gideon Kurada, ya sallami sauraron karar, inda yace masu gabatar da karar sun kasa gabatar da kwararan shaidu akan wanda suke karar.

Sama da shekara hudu, El-Zakzaky da matarsa Zeenat na hannun jami’an tsaro inda ake zargin su akan laifuka guda takwas, da suka hada da kisan kai, tada zaune tsaye, da dai sauran su duka wadanda gwamnatin jihar Kaduna ke zargin su da shi.

Lauyan wanda ake kara, Marshal Abubakar wanda ya wakilci shugaban lauyoyin wanda ake karar a kotun Femi Falana, SAN, ya bayyanawa manema labarai cewa:

Shari’ar Sheikh EL-Zakzaky da matarsa Zeenat ta zo karshe bayan kotu ta wanke su daga laifukan da gwamnatin jihar Kaduna ke tuhumar su da shi.

Kotun ta gano cewa laifin da ake zargin shi da aikatawa a shekarar 2015, ana neman ayi amfani da dokar da aka sanya a shekarar 2017 a yi masa hukunci da ita. Alkalin kotun Gideon Kurada, ya bayyana cewa tun farko ma bai kamata a shigar da wannan kara ba, saboda gwamnati bata da hurumin kama wani akan abinda ba lalifi bane a lokacin.

A karshe kotun tayi watsi da wannan zargi, inda ta wanke El-Zakzaky da matarsa Zeenat, ta kuma bayyana cewa abinda ya faru a ranar 12 ga watan Disambar 2015 zuwa 15 ga watan Disambar 2015, duka ba laifi bane, saboda babu ko daya daga cikin abubuwan da suka faru da za ayi amfani dashi a matsayin laifi akan wadanda ake kara.

Sai dai kuma, lauyan masu shigar da kara, Mr Dari Bayero, yaki amincewa da wannan hukunci, inda a fusace ya fita daga cikinn harabar kotun.

A nashi bangaren, shugaban kungiyar a fannin sadarwa, Ibrahim Musa, ya ce da wannan nasarar da suka samu a kotu, akan laifukan karya da ake zargin shugaban su da matarsa, bayan shafe kusan shekaru biyar a hannunsu, ya ce:

Wannan ya nuna nasara ne akan gaskiya da aminci da muka samu akan azzalumai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe