37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda Abba Kyari ya cika shekaru 47 da haihuwa a hannun jami’an NDLEA

LabaraiYadda Abba Kyari ya cika shekaru 47 da haihuwa a hannun jami'an NDLEA

Shafin sada zumunta Facebook na Kyari ya bayyana cewa an haife shi ne a ranar 17 ga Maris, 1975, Pulse.ng ta ruwaito.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari ya cika shekaru 47 a yau, kamar yadda ya bayyana a shafin sa na sada zumunta na Facebook.

Yadda Abba Kyari ya cika shekaru 47 da haihuwa a hannun jami'an NDLEA
Yadda Abba Kyari ya cika shekaru 47 da haihuwa a hannun jami’an NDLEA

Shafin Facebook na Kyari ya bayyana cewa an haife shi ne a ranar 17 ga Maris, 1975.

Kyari dai yana hannun hukumar ta NDLEA tun bayan da hukumar ta bayyana neman sa akan safarar miyagun ƙwayoyi.

Daga nan ne ‘yan sanda suka kama shi suka miƙa shi ga hukumar NDLEA.

Daga nan ne hukumar ta NDLEA ta shigar da tuhume-tuhume takwas a kan mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, da kuma wasu mutane shida bisa zarginsu da safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta shigar da ƙarar ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu, 2022.

Idan dai ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta tuhumi Kyari da laifin zamba da ya shafi wani fitaccen jarumin Instagram Ramon Abbas aka Hushpuppi da wasu mutane huɗu.

An ce masu damfarar sun hada baki ne wajen sace sama da dala miliyan ɗaya da dubu ɗari daga wani dan kasuwa ɗan ƙasar Qatar.

Laifin ya kai ga dakatar da Kyari kuma an fara bincike na cikin gida, a daidai lokacin da ake kira da a mika shi ga Amurka.

Sai dai kuma an fara shirin miƙa babban ɗan sandan ne a daidai lokacin da Najeriya ta amince da bukatar hukumomin Amurka na miƙa shi.

A karshe dai Abba Kyari ya fito yayi magana, ya bayyana wani boyayyen abu da NDLEA take yi a boye

Abba Kyari, dakataccen mstaimakin kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa gurɓatattun jami’an hukumsr NDLEA ne su kayi masa sharri bayan ya nemi da a bayar da kyauta ga mai tona asiri wanda ya taimakawa ‘yan sandan IRT cafke wanda ake zargi.

Abba Kyari na fuskantar shari’a

Abba Kyari wanda ya ke fuskantar shari’a a wata babbar kotu da ke Abuja bisa zargin sa hannun sa a cikin safarar hodar iblis, ya zargi jami’an NDLEA da bada kariya ga masu safarar kwayoyi zuwa cikin Najeriya. Legit.ng ta rahoto.

Abba Kyari wanda a baya ya ke jagorantar  Intelligence Response Team (IRT) ya fara shiga cikin matsaloli ne tun lokacin da gwamnatin Amurka ta bada sunan shi a cikin wani laifin damfarar yanar gizo.

A yayin da gwamnatin Amurka ta buƙaci da a miƙa mata Kyari, NDLEA ta zarge shi da hannu a cikin safarar ƙwayoyi tare da sauran wasu jami’an ‘yan sanda.

Hukumar ta saki wani faifan bidiyon Abba Kyari yana ƙoƙarin ba ɗaya daga cikin jami’anta cin hanci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

about:blank

Abubuwa 12 masu ban sha’awa game da DCP Abba Kyari, na uku zai bada mamaki

Gwamnatin tarayya ta amince a miƙa Abba Kyari ga Amurka domin fuskantar shari’a

Da duminsa: IGP ya bada umarnin dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin dan sanda

Rubuta Sharhi

Logged in as Haleemah Khaleed.Click to edit your profile Log out »Comment

Sabbin Labarai

Aiko mana da adireshin Email na ku don samun labaran mu da dumi-dumi.GOAccept GDPR Terms

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe