24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

LabaraiBidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

Wata budurwa ta shiga cikin matsanancin tashin hankali kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo tana rusa kuka.

A wani bidiyon TikTok wanda shafin LIB suka wallafa an ga budurwar cike da kunci har tana bayyana cewa shekarun su 6 tare da saurayin.

budurwa
Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa

Ta ce yanzu haka ya yi danwaken zagaye zai aure wata budurwar ta daban wacce mahaifiyar sa ta zaba masa.

Ta ce shekarun su 6 suna soyayya cike da shauki amma duk da haka ya share ta zai sauya akalar soyayyar sa inda ya koma wurin wata daban.

Yanzu haka ta shiga damuwa saboda halin da ta tsinci kan ta duk da soyayyar da suka dade suna yi.

Ga bidiyon a kasa:

Yadda budurwa ta bar saurayinta bayan ya sama mata aiki sannan ya ranci kudi don shirya mata bikin ‘birthday’

Wata budurwa ta bar saurayin ta bayan ya tallafa wa rayuwarta kuma ya yi mata halacci a rayuwa.

An samu bayanai kamar yadda shafin Instablog9ja ta wallafa a Facebook akan wani saurayi da budurwarsa.

Abokin saurayin, wani Michael, mai amfani da @michael_mickyt ne ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya shaida irin cin amanar da aka yi wa abokinsa.

Kamar yadda ya shaida a wallafa:

“An yaudari daya daga cikin abokai na, duk da ya tallafa wurin samar wa budurwarsa aiki wanda tsawon shekaru tana nema ba tare da ta samu ba.

“Bayan wata daya tana aikin ta hadu da wani wanda ta fara soyayya da shi.

“Abunda ya fi bata min rai shi ne yadda ya ranci kudi duk don shirya mata bikin zagayowar ranar haihuwar ta duk saboda soyayya.

“Dama ta tsaya ta biya bashin da ake bin shi kafin ta rabu da shi.

“Abin lura shi ne, yanzu haka sabon saurayin nata a wurin da ta samu aiki yake yin aiki.


Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe