Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, ya caccaki jamiyyar APC wadda ke jagorancin gwamnatin tarayyar Nageriya, akan zargin lalata komai a fadin Najeriya
Muhammad din ya bayyana hakan ne ranar Alhamis 17 ga watan Maris, yayin da yake jawabi a lokacin taron kaddamar da titin Gedu-Oroki-Sabo-Ashipa mai nisan kilomota da digo biyu, 5.2km, dake garin Oyo, a jihar Oyo.
A fadar gwamnan, yace yan Najeriya suna shan wahala, a yayin da kuma

” kabilanci, bangaranci, bambancin addini, kiyayyar addini, da kuma tsantsar son kai a tsakanin mahukunta suka kai matuka a Wannan kasa.”
“Kunga dai abin da APC suka yi sun lalata ko ina a Nageriya. Babu tsaro a ko’ina, Najeriya ta zama babban birnin talauci lamba daya a duniya. An raba kawunan mutane, saboda son rai, an raba su domin wariya, an fusata mutane an saka musu kiyayyar juna.”
Ya fada
Da yake kwatanta APC din jamiyyar sa ta PDP, Muhammad din yace, yanzu PDP din ta bunkasa da samun shuwagabanni masu yaki da
“kabilanci, bangaranci, bambancin addini, kiyayyar addini, wadanda suke kokarin sanya jajirtattun mutane wadanda zasu iya gyara muhalli, wadanda suka san abinda suke yi, wadanda ba yunwar kudi sukeyi ba, wadanda ba zasu zo ne domin su karkatar da albarkatu da kuma wawashe kudaden haraji zuwa aljihunsu ba, a’a mutane ne wadanda suke shirye domin su bude sababbin hanyoyi, su bunkasa tsare-tsare, su kuma gyara tafiyar jagoranci.”
Ya kara da cewa, salon mulki irin na gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, na daga cikin misalin gwamnonin da PDP take alfahari dasu.
Sannan yace, Makinde din ya nuna cewa ya shiga gwamnatin sa ne da tsari, saboda haka ya ci gaba da amfani da duk wasu albarkatu dake hannun sa domin bunkasa rayuwar al’ummar sa.
Ko PDP na so ko bata so sai jam’iyyar APC ta lashe zabe a shekarar 2023 – Mataimakin shugaban majalisar dattawa
Omo-Agegen ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kaddamar da shugabannin kwamatin jamiyyar APC yankin jihar Delta, inda injinya Omeni Sobotie ya zama shugaba Mr Nick Ovuakporie kuma ya zama sakataren sa daga cikin dade-naden da akayi.
Yace, APC ta shirya tsaf domin nukurkusa PDP a jihar Delta, a zaben Shugaban kasa mai zuwa.
Omo-Agege, wanda ya wakilci yankin Delta ta tsakiya, yace aikin kakkabe jamiyyar PDP a Delta babban aikine, inda yaja hankalin yan yan jamiyyar da su jajirce, kuma kada suyi kasa a gwiwa wajen karbar katin jamiyya.
Sanata Agegen ya sami rakiyar Peter Nwaoboshi, Frank Kokori, Olorogun O’tega Emerhor, Chief Austin Izagbo da kuma wadansu shuwagabannin jamiyyar, inda suka nuna murnar su ga wadanda aka nada a mukaman saboda ga kaddamar dasu da akayi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com