24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Hukumar EFCC ta chafke tsohon gwamnan jihar Anambira Willie Obiano sa’o’i kadan bayan murabis daga kujerar Gwamna

LabaraiHukumar EFCC ta chafke tsohon gwamnan jihar Anambira Willie Obiano sa'o'i kadan bayan murabis daga kujerar Gwamna

Hukumar EFCC ta na zargin sa da laifin cin hanci

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Anambira, Willie Obiano, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Wasu majiyoyi daga hukumar wanda suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana da manema labarai a kan lamarin, sun ce an damke tsohon gwamna mista Obiano ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke garin Legas, a lokacin da ya ke shirin shiga jirgi zai bar kasar zuwa Houston dake kasar Amurka.

An ce an kama shi ne da misalin karfe 8:30 na dare. ranar Alhamis.

EFCC ta ce Mista Obiano ya dade yana cikin jerin sunayen Da hukumar ta EFCC ke nema.

EFCC a yau 17 ga watan Maris, 2022 ta kama tsohon gwamnan jihar Anambra Obiano. Tsohon gwamnan wanda dama ya dade cikin jerin sunayen da hukumar ke hara, an chafke shi ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 8:30 na dare a lokacin da yake shirin shiga jirgi zuwa birnin Houston na kasar Amurka,” wata majiya ta shaida wa jaridar PREMIUM TIMES.

Ba a kashe wata wutar ba wata wutar ta kunno kai

Har zuwa lokacin da aka kama tsohon gwamna, ba a gama kashe wutar hatsaniyar da ta kunno kai ba a yayin da matar marigayi Ojukwu ta zabgawa, matar tsohon gwamna mari,, a wurin bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Anambra.

Duk da cewa ba a iya tantance cikaken bayanan zargin da EFCC ke yi wa Mista Obiano ba a ranar Alhamis, amma za a tuna cewa tun a shekarar da ta gabata ne hukumar ta sanya tsohon gwamnan a jerin sunayen da take fako.


EFCC ta dade da daura idonta akan tsohon gwamna

PREMIUM TIMES ta ruwaito a watan Nuwambar shekarar da ta gabata cewa Hukumar EFCC ta aike da wata wasika zuwa ga Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021,in da ta bukaci Hukumar da ta sanya Gwamnan a cikin jerin sunayen da suke fako kuma a sanar da hukumar duk ranar da aka hange shi zai bar kasar.
Ba bu cikaken bayanin dalilin da ya sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta rattaba sunan gwamnan cikin jerin sunayen da su ke fako.

Sai dai wasu majiyoyi masu kaifin basira sun shaida wa wannan Jaridar Premium Times cewa matakin chafke shi na nuni da cewa hukumar ta dade tana bincike a hankali kan gwamnan kuma ta yiwu ta samu bayanan sirri cewa ya shirya barin kasar bayan ya mika ragamar mulki ga wanda zai gaje shi.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun yi masa dirar mikiya a ranar Alhamis sa’o’i kadan bayan ya rasa kariyar mulki da ke katangeshi daga tuhumar sa da aikata laifuka a lokacin da yake rike da madafen iko.

Taro ya bar baya da kura:An rasa gane waye ya mari wani tsakanin matar tsohon gwamna da matar marigayi Ojukwu a wurin taron rantsar da sabon gwamnan jihar Anambira

Taro ya zama filin dambe

Abu kamar wasan kwaikwayo,a yau Alhamis a wurin bikin rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambira lokacin da uwargidan gwamnan mai barin gado Willie Obiano, Ebelechukwu ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen taron.

Misis Ojukwu ita ce matar marigayi jagoran Biafra, Odumegwu Ojukwu.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da ke wajen taron ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan da aka rantsar da Mista Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambira.

NAN ta ruwaito cewa manyan baki da suka hada da Mista Obiano gwamna mai murabus suna zauna a lokacin da Mrs Obiano ta taho gaba gadi ta tunkari inda matar marigayi Ojukwu ke zaune ta zabga mata mari.

Jam’ian tsaro sun farga da faruwar lamarin

Fauwar lamarin ya ja hankalin jami’an tsaro da sauran mutane inda suka yi kokarin janye Misis Obiano daga hannun Misis Ojukwu wanda hakan yabar mutane da sakin baki.
Misis Obiano aka sata a mota aka dauketa da ga wurin taron, tafiyar ta ba dadewa,shima mijin ta ya bar wurin tun da yariga ya mika ragamar mulki ga sabon gwamna.

A wani labarin kuma an sami rahoton cewa Matar marigayi Ojukwu ita ta sharawa matar gwamna mai murabus mari

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa Bianca Ojukwu ce ta mari matar tsohon Gwamna Willie Obiano, Ebelechukwu, a wajen bikin rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambra.
Dalilin da ya sa akayi zaton cewa Misis Obiano ita ce ta mari matar Ojukwu saboda an hange ta ta tashi daga kujerar da ta ke zaune ta tunkari inda Misis Ojukwu ta ke, shi yasa mutane da dama ciki har da ‘yan jarida suka dauka cewar ita Matar tsohon gwamna ne ta mari matar Ojukwu.koma dai mai ya faru Allah ya kauda shaidan.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe