27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Watarana zamu koma kan ka, Sojojin Rasha sun ja kunnen Putin akan sanya su ta’addanci ga kasar Ukraine

LabaraiWatarana zamu koma kan ka, Sojojin Rasha sun ja kunnen Putin akan sanya su ta’addanci ga kasar Ukraine

Sojojin Rasha da aka kama a Ukraine sun gargaɗi Vladimir Putin cewa wata rana za su dawo kansa bayan an sanya su kai hare-haren ta’addanci a Ukraine.

Sojojin sun yi Allah wadai da harin bam da aka kai a wani asibitin haihuwa a birnin Mariupol a ranar 9 ga watan Maris. 

Sojojin sun gargaɗi Putin

Yayin da su ke magana da CNN, matuƙan jirgin guda uku sun gargaɗi Putin cewa ‘ba za ka daɗe kana boyewa daga wannan ba’ saboda sojoji da yawa su na da ra’ayi irin na mu kuma nan ba da daɗewa ba za mu dawo gida. Shafin Lindaikejiblogspot.com ya rahoto

Sun ɗora alhakin akan kwamandojin sojojin Rasha bisa munanan laifuka akan yan ƙasar Ukraine, inda su ka yi gargaɗin cewa wannan ba abin da zaa iya yafewa ba ne. 

Sojojin sun yi tir da harin

Ban san wanda zai iya kare wannan ba, hawayen ƙananan yara, ko abinda yafi muni mutuwar mutanen da ba su da haƙƙi waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba. A cewar Maxim sojan saman Rasha.

Wannan ba kawai cin galaba akan sojojin Ukraine ba ne, amma yanzu ana tarwatsa mutane.

Wannan furucin ya ƙara ƙarfin maganganun da sojojin Rasha su ka yi da dama bayan an kama su a ƙasar Ukraine. Sai dai masu lura da al’amura na ganin cewa tursasu ake yi su na juya baya ga ƙasar su ta Rasha.

Sai dai CNN ta rahoto cewa matuƙan guda uku ba su yi magana cikin tsoro ba inda ba sanya mu su ankwa ba kuma ba ana faɗa musu abinda za su faɗa ba ne.

Hakan na zuwa ne dai bayan Rasha ta jefa bam a wani asibitin ƙarbar haihuwa ranar 9 ga watan Maris a birnin Mariupol inda mutum huɗu su ka rasa rayukan su, ciki kuwa har da wata mata mai ɗauke da juna biyu wacce jaririnta shi ma ya mutu kwanaki kaɗan bayan harin.

Sojojin Rasha sun tarwatsa wani masallaci da mutum 80 suka boye a ciki a kasar Ukraine

Sojojin Rasha sun gargaje wani masallaci da ke kudancin Ukrainian port city of Mariupol, inda fiye da manya 80 da yara suka fake, kamar yadda ma’aikatar harkokin kasashen waje na Ukraine ya bayyana a ranar Asabar, Aljazeera ta ruwaito.

Ma’aikatar ta bayyana hakan a Twitter cewa ‘yan kasar Turkiyya da dama suna cikin wadanda suka fake a masallacin wanda aka sa wa abubuwa masu fashewa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe