24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Bidiyon wata mata yayin da take gwangwaje mijin ta da mota mai kimar N87m ya dauki hankula

LabaraiBidiyon wata mata yayin da take gwangwaje mijin ta da mota mai kimar N87m ya dauki hankula

Wata mata mai ɗauke da juna biyu wacce ake sa ran haihuwarta kwanan nan, sannan ta wuce hutun bangali na al’ada ta yi wa mijin ta kyautar mota ƙirar Lamborghini Huracan Evo wacce ta kai zunzurutun kuɗi har miliyan 87 (N87m)

Mijin zai cigaba da ɗawainiya

A lokacin da Anes Ayuni Osmanis, 19, za ta haihu cikin wannan watan, mijin ta Weldan Zulkefli shine zai cigaba da kulawa da jaririn ta yadda matar sa za ta murmure. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Wannan al’ada ce kuma hutun na bayan haihuwa yana ɗaukar kwanaki ɗari. A cikin waɗannan kwanakin mijin shine zai cigaba da kula da lamura.

Kyauta bisa sadaukarwar sa

A matsayin kyautar sadaukarwar da Zulkefli zai yi a cikin kwanaki ɗarin hutun da matar sa za ta yi, matar sa ta yi masa wata gagarumar kyautar bazata. Ta miƙa masa mota cikin shaukin ƙauna a cikin wani bidiyo da aka wallafa a Tiktok.

A cikin bidiyon, ta rufe wa mijinta fuska sannan ta kai shi zuwa shagon mai sayar da motoci inda ta bashi wannan kyautar.

A lokacin da ta ke wallafa bidiyon, ta rubuta cewa:

Nagode mijina, duk girman darajar wannan kyautar ba za ta iya biyan kyautatawar ka ba.

Kalli bidiyon a wannan link ɗin

Ango ya fashe da kukan murna bayan amarya ta bashi kyautar dalleliyar mota a wajen daurin auren su

Wata mata ‘yar Najeriya ta yi abinda ba kasafai aka fiya yin shi a kasar ba, hakan ya sanya mutane suke ta faman tofa albarkacin bakin su akan wannan abu da tayi.

Amaryar dai ta yi abin a yaba mata, domin kuwa a ranar daurin aurensu ta fito da makullan sabuwar mota ta bawa angon nata kyauta.

A wani dan matsakaicin bidiyo da Gossip Mill Nigeria ta wallafa a shafinta, an nuno angon cikin wani yanayi na tsoro yayin da ya hango amaryar ta tinkaro shi, amma daga baya lamarin sai ya zame masa abin mamaki.

Cikin rashin sanin abinda zai faru, sai ya bata rai, inda su kuma abokanan shi suka fara tsokanar shi. Wani can daga bayan shi yana cewa wannan bai san abinda ke shirin faruwa ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe