24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Babu abinda yake sa ni bakin ciki kamar in na tuna zan mutu in tarar da Allah, Jaruma Maryama Yahaya

LabaraiKannywoodBabu abinda yake sa ni bakin ciki kamar in na tuna zan mutu in tarar da Allah, Jaruma Maryama Yahaya

Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Yahaya yayin zantawa da BBC Hausa ya shaida cewa babu abinda ya fi bakanta mata rai kamar ta tuna cewa watarana zata mutu ta tarar da Allah.

Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne jarumar ta yi wani gagarumin ciwo wanda yasa ta fita daga hayyacin ta har wasu suka dinga tunanin mutuwa zata yi.

maryama yahaya
Babu abinda yake sa ni bakin ciki kamar in na tuna zan mutu in tarar da Allah, Jaruma Maryama Yahaya

Ciwon ya yi matukar sauya mata halitta har ta kai ga wadanda suka san ta basa gane ta, yanzu haka dai ta warke sarai tamkar bata taba ciwo ba.

A ranar Alhamis, 17 ga watan Maris a wani bidiyo wanda BBC Hausa ta wallafa na tattaunawar da aka yi da ita ta bayar da takaitaccen tarihin ta.

Kamar yadda tace:

“Ni dai sunana Maryam Yahaya, an haife ni a garin Kano, Anguwar Goron Dutse.”

Ta ci gaba da cewa ta yi karatun firamare da sakandare, sannan tun tana karama ta ke sha’awar fara fim wanda yanzu haka take gode wa Allah akan fim din da ta ke yi.

Ta ce ta fara fim a shekarar 2016 wanda ta fara da fim
din ‘Masur’ kuma a yanzu haka bata san yawan fina-finan da ta yi ba kuma duk tana son su sosai.

Yayin da aka tambaye ta abinda yake sa ta farin ciki cewa ta yi:

“Gaskiya abinda ya ke sa ni farin ciki abu ne guda daya. Babu abunda yake saka ni farin ciki kamar in ga iyaye na da ‘yan uwa na cikin farin ciki.”

Yayin da aka tambaye ta abinda yake saka ta bakin ciki sai ta kada baki tace:

“Babu abunda yake saka ni bakin ciki irin in tuna cewa wata rana zan mutu in koma ga Ubangiji na.”

Dangane da abincin da ta fi so ta ce Tuwo miyar kubewa danya, kuma ta ce bata da babbar kawa a Kannywood, mahaifiyar ta ce babbar kawar ta.

Ta ce a Kannywood tana da yayyi mata, iyaye da kuma kawaye masu ba ta shawara.

Ta ce kasashen da ta taba zuwa sun hada da Saudiyya, Dubai, Gambia, Nijar da sauran su.

Ta ce tana burin ta rabu lafiya da duk ‘yan Kannywood ta kuma yi aure. Kuma tana da burin yin siyasa.

Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

A ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairun 2022 jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ta saki sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram ba tare da ta sanya rigar mama ba.

Hotunan sun janyo mata suka da caccaka ko ta ina kafar inda wasu suka dinga zagin ta akan yadda bata dade da murmurewa daga ciwo ba ta fara shigar banza.

Wasu sun dinga yi mata wa’azi suna cewa ya kamata ta yi wa kanta fada ta daina duk wasu ayyuka marasa kyau musamman ganin ko jikin ta bata gama mayarwa ba.

A kwanakin baya jarumar ta yi ciwo wanda mutane da dama suka zaci mutuwa zata yi don duk ta rame ta fita hayyacin.

A lokacin, masoyanta sun dinga yi mata fatan alkhairi da kuma fatan zata natsu, ciwon ya zama izina a gare ta ta gyara rayuwar ta.

Ba wannan bane karon farko da jarumar ta saba yin hotuna ba tare da ta sanya rigar mama ba. Ga masu bibiyarta a Instagram, ta kan saki bidiyoyi ko kotuna sanye da riguna da suke tabbatar da hakan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe