35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ana kulla kullalliyar hana Atiku, Saraki da Tambuwal fitowa takara a jam’iyyar PDP

LabaraiAna kulla kullalliyar hana Atiku, Saraki da Tambuwal fitowa takara a jam'iyyar PDP

Sarkakiya ta balle a jam’iyyar PDP yayin taron jiga-jiga wanda aka yi a daren Litinin, hakan ya sa shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorcha Ayu ya yi gaggawar dakatar da taron zuwa yau, The Nation ta ruwaito.

Hayaniyar ta samo asali ne bayan wasu shugabanni daga kudu suka fara batun cewa a cire mambobin da suka koma APC a baya sannan suka kara dawowa PDP daga cikin jerin wadanda zasu tsaya takarar shugaban kasa.

su atiku
Ana kulla kullalliyar hana Atiku, Saraki da Tambuwal fitowa takara a jam’iyyar PDP

Wani gwamnan kudu kamar yadda majiyoyi suka bayyana ya amince da wannan batu.

Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da kuma gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal suna daga cikin sanannun mutanen da suka bar jam’iyyar PDP zuwa APC don su tsaya takara a zaben 2015.

Sai dai sun kara komawa PDP bayan sun kasa zama inuwa daya da fadawan Muhammadu Buhari da kuma shugabannin APC.

Wasu daga cikin su sun ci zabe yayin da wasu suka fadi a zaben 2019 karkashin jam’iyyar PDP.

Duk suna harin tsayawa takarar shugaban kasa.

Wadanda suka kawo batun cire masu sauya shekarar sun tsaya akan cewa komawar su APC ne ya janyo jam’iyyar PDP ta fadi zabe a 2015.

Sun ce PDP ta shiga mawuyacin hali ne saboda abinda wadannan mutane suka yi.

Sannan mutanen kudun sun tsaya akan cewa wajibi ne a ba wa dan kudu damar tsayawa takara inda suka ce faduwa zaben da Goodluck Jonatha ya yi a 2015 ya yi sanadiyyar mutane suka dinga barin PDP.

Amma duk da haka wasu mambobi daga arewa sun nuna rashin amincewar su akan wannan batu, inda suka ce babu dalilin da zai sa a cire wadanda suka koma jam’iyyar bayan sauya sheka.

Wata majiya da ta halarci taron ta ce:

“Duk mun san wadannan su ne suka tsaya takara a 2019 karkashin inuwar PDP bayan dawowa jam’iyyar mu mai albarka.

“Idan babu wanda ya hana takara a 2019, wacce hujja zata sa a hana su takara?

“Abin ban takaici ne yadda wasu suke yi kamar PDP jam’iyya da suka kafa ne da kan su.

“Ya kamata mu gane cewa akwai wadanda su suka gina jam’iyyar har ta kai wannan matakin. Don haka mutane su daina yin kamar su ne masu jam’iyyar. Kowa yana da damar da zai taka rawar sa.”

Ya ci gaba da bayani inda yace hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin PDP na 199 wanda ya ja kunne akan hana wani dan jam’iyya takara.

Wata majiya ta shaida wa The Nation cewa ana fara hayaniyar Dr Ayu ya kawo karshen taron.

2023:Jam’iyyar PDP ta fitar da jaddawalin Kudaden Tikitin takarar kowace kujera

Jam’iyyar ta amince da hakan ne a babban taron jam’iyyar na kasa karo na 95 da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.

Haka kuma, ‘yan takarar majalisar wakilai za su biya Naira 2.5, tare da kudin nuna sha’awar takara Naira 500,000 sai kudin tikitin tsayawa takara a kan N2m.

Masu neman takarar majalsar dokokin jiha

Masu neman takarar majalisar dokokin jiha za su biya Naira 100,000 kudin sha’awar tsayawa takara da kuma Naira 500,000 na tikitin tsayawa takara.
Hakazalika jam’iyyar ta amince da rage kashi 50 cikin 100 na kudaden takara ga matasa da basu wuce shekaru 25 zuwa 30 na mukamai daban-daban.

Hukumar zabe ta kasa(NEC) ta kuma amince da kafa kwamitin shiyya mai wakilai mutum 37 domin bayar da shawarwarin yadda za a ware mukamai daban-daban na zaben shekarar 2023.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe