24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Taro ya bar baya da kura:An rasa gane waye ya mari wani tsakanin matar tsohon gwamna da matar marigayi Ojukwu a wurin taron rantsar da sabon gwamnan jihar Anambira

LabaraiTaro ya bar baya da kura:An rasa gane waye ya mari wani tsakanin matar tsohon gwamna da matar marigayi Ojukwu a wurin taron rantsar da sabon gwamnan jihar Anambira
Ebele Obiano and Bianca Ojukwu
An rasa gane waye ya mari wani tsakanin matar tsohon gwamna da matar marigayi Ojukwu

Taro ya zama filin dambe

Abu kamar wasan kwaikwayo,a yau Alhamis a wurin bikin rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambira lokacin da uwargidan gwamnan mai barin gado Willie Obiano, Ebelechukwu ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen taron.

Misis Ojukwu ita ce matar marigayi jagoran Biafra, Odumegwu Ojukwu.

Pic 2 Prof Chukwuma Soludo takes over as Governor of Anambra 768x576 1
Sabon gwaman jihar Anambira a yayin da ake rantsar da shi

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da ke wajen taron ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan da aka rantsar da Mista Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambira.

NAN ta ruwaito cewa manyan baki da suka hada da Mista Obiano gwamna mai murabus suna zauna a lokacin da Mrs Obiano ta taho gaba gadi ta tunkari inda matar marigayi Ojukwu ke zaune ta zabga mata mari.

Jam’ian tsaro sun farga da faruwar lamarin

Fauwar lamarin ya ja hankalin jami’an tsaro da sauran mutane inda suka yi kokarin janye Misis Obiano daga hannun Misis Ojukwu wanda hakan yabar mutane da sakin baki.

Jim kadan da faruwar lamarin aka janye Misis Obiano aka sata a mota aka dauketa da ga wurin taron, tafiyar ta ba dadewa,shima mijin ta ya bar wurin tun da yariga ya mika ragamar mulki ga sabon gwamna.

A wani labarin kuma an sami rahoton cewa Matar marigayi Ojukwu ita ta sharawa matar gwamna mai murabus mari

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa Bianca Ojukwu ce ta mari matar tsohon Gwamna Willie Obiano, Ebelechukwu, a wajen bikin rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambra.
Dalilin da ya sa akayi zaton cewa Misis Obiano ita ce ta mari matar Ojukwu saboda an hange ta ta tashi daga kujerar da ta ke zaune ta tunkari inda Misis Ojukwu ta ke, shi yasa mutane da dama ciki har da ‘yan jarida suka dauka cewar ita Matar tsohon gwamna ne ta mari matar Ojukwu.koma dai mai ya faru Allah ya kauda shaidan.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe