22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Sojojin Rasha sun tarwatsa wani masallaci da mutum 80 suka boye a ciki a kasar Ukraine

LabaraiSojojin Rasha sun tarwatsa wani masallaci da mutum 80 suka boye a ciki a kasar Ukraine

Sojojin Rasha sun gargaje wani masallaci da ke kudancin Ukrainian port city of Mariupol, inda fiye da manya 80 da yara suka fake, kamar yadda ma’aikatar harkokin kasashen waje na Ukraine ya bayyana a ranar Asabar, Aljazeera ta ruwaito.

Ma’aikatar ta bayyana hakan a Twitter cewa ‘yan kasar Turkiyya da dama suna cikin wadanda suka fake a masallacin wanda aka sa wa abubuwa masu fashewa.

ukraine muslims
Sojojin Rasha sun tarwatsa wani masallaci da mutum 80 suka boye a ciki a kasar Ukraine

Kamar yadda wallafar ta nuna:

“Sojojin Rasha sun tarwatsa Masallacin mai girma Sultan Suleiman da matarsa, Roxolana (Hurrem Sultan) da ke Mariupol.

“Fiye da mutane manya 80 da yara sun fake a cikin sa suna zama ciki har da ‘yan kasar Turkiyya.”

Ba ta bayyana ko an halaka mutanen ba ko kuma an ji musu raunuka.

Moscow ta musanta kai wa fararen hula farmaki inda tace fada ne tsakanin sojojin ta da na Ukraine.

Ukraine ta zargi kasar Rasha da kin barin mutane su fita daga Mariupol, inda daruruwan mutane suka makale. Rasha tana zargin Ukraine da kin kwashe mutane.

Mariupol tana cikin mawuyacin hali inda ake ta auna bama-bamai fiye da makwanni biyu kuma sojojin Rasha sun zagaye ta.

Lamarin ya cakude wanda ya janyo fararen hula sun shiga tashin hankalis suna kokarin ganin sun fita saboda rashin kayan abinci.

Kamar yadda ministan harkokin kasashen waje na Ukraine ya wallafa a Twitter ranar Juma’a:

“Annobar Mariupol ita ce mafi munin annoba a baya kasa, wacce ta halaka fararen hula 1,582 a cikin kwana 12.”

Elon Musk da Jeff Bezos sun tafka asarar tiriliyan N7.4 a rana ɗaya a dalilin rikicin Rasha da Ukraine

Mutum biyu daga cikin masu arziƙin duniya, Elon Musk da Jeff Bezos sun tafka asarar tiriliyan N7.4 a rana ɗaya biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine.

Elon Musk da Jeff Bezos Sun tafka babbar asara

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, tattalin arziƙin sa ya dawo dala biliyan $199 ($199 billion) bayan ya tafka asarar dala biliyan $13 ($13 billion).

Jeff Bezos, mutum na biyu cikin jerin masu arziƙin duniya kuma mai kamfanin Amazon, ya tafka asarar dala biliyan $5.41 inda tattalin arziƙin sa ya dawo dala biliyan $169.

Faɗuwar kadarorin su ta zo ne bayan an sanar da cewa sojojin Rasha sun fara tada bama bamai a wasu yankunan ƙasar Ukraine, wanda hakan ya sanya ɗar-ɗar a cikin kasuwanni. Ƙasuwar crypto tayi ƙasa sosai a safiyar Alhamis 24 ga watan Fabrairun 2022. Farashin ɗanyen man fetur yayi tashin gwauron zabi zuwa $100 kan kowace ganga.

Farashin ɗanyen mai ya ƙaru

An sayar da ɗanyen mai kan farashin $95 kowace ganga a wasu lokuta yayin hada-hadar kasuwanci a ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairun 2022.

An sayar da shiyar kamfanin Tesla akan dala $764.04, inda ta ragu da kaso 7 kan yadda aka sayar da ita a kasuwar baya. Sai dai darajarta ta ƙaru inda ta samu ƙarin kaso 2.91% inda aka sayar da ita kan dala $787.27 

Ana hasashen cewa darajar kasuwanni za ta cigaba da faɗuwa yayin da rikicin ƙasashen Rasha da Ukraine ke ƙara ƙamari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe