24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Dalilin da ya sa na yi zanga-zanga ana tsaka da shari’ar Kyari, Jarumi Zaharadeen Sani

LabaraiDalilin da ya sa na yi zanga-zanga ana tsaka da shari’ar Kyari, Jarumi Zaharadeen Sani

Fitaccen jarumin Kannywood, Zaharadeen Sani, ya ce yana harabar babbar kotun tarayya ranar Litinin akan kin bayar da belin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da ake kan shari’ar shi, Premium Times ta ruwaito.

Kyari yana fuskantar tuhuma akan laifuka da dama ciki jar da safarar hodar iblis.

zahradeen sani
Dalilin da ya sa na yi zanga-zanga ana tsaka da shari’ar Kyari, Jarumi Zaharadeen Sani

Kyari da sauran wadanda ake tuhuma sun bayyana a kotun ranar Litinin don gabatar da bukatar belin su gaban alkali, Emeka Nwite.

Yayin wata tattaunawa da Premium Times a ranar Talata, Sani ya ce ya je kotu a ranar Litinin don yin zanga-zanga akan kin bayar da belin Kyari da kotun ta yi.

Kamar yadda yace:

“Na yarda da abubuwan da yake yi wa kasar nan da kuma ni, ina tunanin ya cancanci a bayar da belin shi. Na yi abinda na yi a kotun ne don jama’a su gane cewa muna tare da shi kuma ya cancanci beli.

“Zamu kara komawa wani zaman kotun da shirin zanga-zangar mu.”

Sani ya yi fice ne a fim din sa mai suna ‘Abu Hassan’ wanda ya bayar da labari akan ta’addanci da Boko Haram a Najeriya.

Furodusa ne, jarumi ne kuma darekta a masana’antar Kannywood.

Ja’afar Ja’afar, Barista Bulama Bukarti da sauran su sun yi zanga-zanga a birnin Landan, sun ce Buhari ya gaza

‘Yan Najeriya da ke zama London sun fita zanga-zanga inda suka ce Buhari ya gaza sakamakon rashin tsaro da ya addabi arewacin Najeriya.

A ranar Alhamis, fitaccen lauya mai aiki da cibiyar Tony Blair, Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana a wani bidiyo na Facebook kai tsaye yayin zanga-zanga a birnin Landan.
A cikin wadanda su ka yi zanga-zanga kan gazawar Buhari har da Jaafar Jaafar, fitaccen dan jaridar nan na jihar Kano mai jaridar Daily Nigerian tare da sauran mutane inda suka dinga caccaka tare da suka akan lamarin da ke aukuwa a Najeriya.

A cewarsu, ko dai Buhari ya yi gyara akan rashin tsaron da ya addabi Najeriya ko kuma ya yi murabus.
Yayin zanga-zangar, cikin fushi da takaici Barista Bukarti ya ke cewa rayukan ‘yan arewa sun zama tamkar na kiyashi, kullum halaka su ake yi.
Yayin da manema labarai su ka bukaci jin dalilin zanga-zangarsu a birnin Landan, Barista Bukarti ya ce ya kamata duk inda Dan Najeriya yake ya kasance mai kishin kasarsa.


“Jami’an tsaro su na ta harbe masu zanga-zangar lumana a Najeriya don ko jiya sun halaka mutane biyu. Hakan yasa mu ka ga ya dace mu yi zanga-zangar a nan don kowa ya san halin da Najeriya ta ke ciki,” a cewarsa.


Ya kara da bayyana cewa basu san ranar da za su dakata da zanga-zangar ba. Ya ce sai ranar da suke ganin Buhari ya samar da gyara a tsaro sannan zasu iya tsagaitawa don abin ya yi yawa.
Nan da nan mutane da dama su ka garzaya karkashin bidiyon nasu na kai tsaye wanda ya kwashe sa’o’i ana yi su na kara musu kwarin guiwa tare da yi musu fatan alkhairi.
‘Yan Najeriya sun nuna cewa su na tare da su dari bisa dari don hakan zai iya kawo sauki daga matsalolin tsaron da Najeriya ta ke fuskanta, a ganin wasu.
Duk da dai akwai wadanda su ka dinga kushe su na nuna cewa zanga-zangar ba ta da wani amfani, amma kai tsaye, fiye da mutane dubu biyu sun ci gaba da bibiyarsu ta bidiyon na Facebook wanda a agogon Najeriya su ka fara tun kafin karfe 1 na rana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe