24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da yawan gaske yayin da suke tsaka da shagalin bikin shugabansu a Katsina

LabaraiSojoji sun kashe 'yan bindiga da yawan gaske yayin da suke tsaka da shagalin bikin shugabansu a Katsina

‘Yan bindiga da dama sun rasa rayukan su yayin da sojojin sama, NAF suka dinga ragargazar su yayin da suke bikin daya daga cikin shugabannin su a Jihar Katsina, Jaridar Leadership ta ruwaito.

Cikin wadanda aka halaka har da Sule, wani shu’umin dan bindiga, wanda dan uwan Lalbi Ginsha ne, shi ma gagarumin dan ta’adda ne.

fighter jet
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da yawan gaske yayin da suke tsaka da shagalin bikin shugabansu a Katsina

Kamar yadda PRNigeria ta ruwaito, lamarin ya auku ne a kauyen Unguwar Adam da ke karamar hukumar Dan Musa a Jihar Katsina.

Majiyar sirri ta bayyana yadda sojojin saman suka samu bayanan sirri akan cewa ‘yan bindiga sun bar Dan Alikima zuwa Unguwar Adam don shagalin bikin wani shugaban su.

“Hakan yasa sojojin saman suka shirya tsaf a jiragen su don yi wa yankin aman wuta. Daga bisani aka samu labarin cewa fiye da ‘yan bindiga 50 da suka je bikin sun rasa rayukan su.

Kamar yadda jami’an suka bayyana, jirgin samar sojin yana ta zagaye yankin kuma inda ya bi su har zuwa sabon wurin da suka koma, wato kusa da wani rafi da ke arewacin Unguwar Adam.

Sannan wata majiya ta sanar da PRNigeria cewa ‘yan bindiga da dama sun raunana yayin da wasu suka rasa rayukansu.

A cewar majiyar:

“Yan bindiga fiye da 27 sun rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka ji raunuka. Cikin wadanda aka halaka har da Sule, dan uwan babban dan bindigan nan, Lalbi Ginshima.”

Karshen ‘yan bindiga ya zo – Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 150 da ruwan bama-bamai a jihar Zamfara

A ranar Alhamis ne helkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar sojin sama ta “Operation Hadarin Daji,” sun kashe akalla ‘yan bindiga 123 a jihar Zamfara.

Ta kara da cewa sojojin sun tarwatsa maboyar ‘yan bindigar a kudancin garin Dansadau, arewa da dajin Kuyambana, da kuma arewacin dajin Sububu da kuma kauyen Dudufi, dake cikin karamar hukumar Maradun.

Mukaddashin Daraktan, kafafen yada labarai, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana haka a lokacin da yake bayar da bayani kan kokarin da sojoji ke yi a fadin kasar nan cikin makonni biyu da suka gabata.

Ya ce:

Tsakanin 2 zuwa 6 ga watan Agustan 2021, rundunar sojin sama ta “Operation Hadarin Daji”, ta kai munanan hare-hare ta sama kan maboyar ‘yan bindiga a kudancin garin Dansadau’ arewacin dajin Kuyambana, da arewacin dajin Sububu da kauyen Dudufi karkashin gundumar Faru dake karamar hukumar Maradun, duka a cikin jihar Zamfara.

Mayakan Boko Haram 45 sun mika wuya ga hukumar soji

Harin ‘yan bindigar ya yi sanadiyyar lalata sansanin ‘yan bindigar ciki hadda gidan wani shugabansu, Halilu Tubali, inda ‘yan bindigar suka taru don yin taro.

Hare-haren da aka kai musu ta sama da ta kasa ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 123 da kuma lalata kayayyakin aikinsu.


Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Punch

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe