24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Sautin kiran Sallah ya zama abu mafi dadin saurare da kungiyar mu ta saurara a kasar Pakistan – Cewar Pat Cummins

LabaraiSautin kiran Sallah ya zama abu mafi dadin saurare da kungiyar mu ta saurara a kasar Pakistan - Cewar Pat Cummins

Pat Cummins yayi farin cikin kasancewar sa cikin tawagar kwararru ‘yan wasa na kasar Australia  yayin   ziyarar  yawon bude ido da suka je kasar Pakistantan bayan shekara 25 rabonsu da kasar. 


A fadar Cummins din wannan ziyarar tasu mai dimbin tarihi, ta musamman ce shi a gareshi. Dan wasan, wanda ya jagoranci wakilci Australia a jerin gwaje-gwaje ya kira ziyarar da ” ta musamman ” a rayuwar sa da kuma rayuwar sana’ar sa. 


Har’ila yau dai, dan shekara 28 din, ya sake nuna wata gajiyar da yaci, a yayin ziyarar da tawagar Australia din suka kai kasar, a duk lokacin da suka ji kiran sallah. 

cummins
Sautin kiran Sallah ya zama abu mafi dadin saurare da kungiyar mu ta saurara a kasar Pakistan – Cewar Pat Cummins

Cummins din ya bayyana cewa yanayin ” Mai sanyi ” yana kasancewa a duk lokacin da duk yan kungiyar suka gusa, idan aka fara KIRAN SALLAH, wanda yake karade daukacin filin wasan kwallon kiriket na Rawalpindi, wanda suke jiyo sautin daga can nisan saman wasu tsaunuka. 


Yace, nishadin da yake samu a wannan yanayin ya zarce na kowanne irin  lokacin da suke, shafewa yayan gudanar da horon su. 


Kaftin din na kungiyar Ashes winning, ya bayyana cewa, kungiyar tasa suna ta gwagwarmayar gasar gwaji ne da yanzu haka ake aiwatarwa kuma suna yin duk mai yiwuwa domin zama na gabagaba wajen lashe lambobin kambi dake filin wasan kwallon kiriket na Pindi.


 Ya kara da cewa, yan kungiyar wasan ta Australia ta ji dadin gamuwa da sa’anni matasa manyan gobe a wasan kwallon kiriket, a kasar Pakistantan, wadanda basu taba ganin wasan kiriket mai armashin wanda akayi a yanzu ba a gidan su. 


Cummins din ya yabawa mahukunta da kuma duk ma’aikatan da suka taimaka wa ziyarar tasu. Yayi godiya ga jami’an tsaro, inda yace sun taimaka wajen baiwa yan kungiyar tasa kariya yadda ya kamata. 


A karshe Cummins ya bayyana ziyarar da cewa, wani mahimmin darasi ne ga duk wadanda suka halarci tafiyar, a rayuwar su domin a cewar sa mai yiwuwa wannan ce damar mutum ta karshe da zai halacci kasar a tsawon rayuwar sa.

Za a dinga cin tarar Naira 100,000 ga duk wanda ya kunna waka a lokacin da ake kiran Sallah a Saudiyya

Kasar Saudi Arabia, ta Sanya tarar Riyal dubu daya 1000 SR, ga duk wanda ya kunna kida, yayin da ake kiran sallah. Ana yin kiran sallah ne sau biyar a ko wacce rana a cikin amsa kuwwa. ( laasfika ). 

An gabatar da sabbin tarar ne jim kadan bayan ministan cikin gida Abdulaziz Bin Saud Bin Naif, ya fitar da dokar hukumar, wadda take nuna sauyi ga kyawawan dokokin zamantakewa. 

Tarar Riyal dubu daya 1000 ko 2000

Duk wanda aka kama ya kunna kida yayin da ake yin kiran sallah, to za’a ci tarar sa Riyal dubu daya 1000. Idan kuma ya sake, to tarar zata lunku zuwa dubu biyu 2000.

Dokar za ta hau kan duk wanda ya kure kida yayin kiran sallah ne kadai, da kuma duk wanda ya kure kida a cikin motarsa ta hawa, ko kuma a cikin gidajen mutane. 

Tarar Ryal dari biyar 500 idan makoci ya kai karar ka

Bugu da kari kuma, kasar Saudiyya ta sanya karin tara akan duk wanda ya kure kida a cikin gidan sa ya takurawa makwafta, idan har makwaftan suka kai korafi, to zai biya tarar Ryal dari biyar 500. 

Mutane suna kunna kida a waya a Ka’abah

A fadar gwamnatin kasar, ana ganin mahajjata na cikin kasar, ko wadanda suka zo daga wasu kasashen, suna amfani da wayoyinsu na hannu a lokacin da ake yin kiran sallah, wanda yin hakan ya saba da da’a kuma haramunne. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe