27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

2023:Gwamna Aminu Tambuwal ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su sake su zabi dan takarar da ya haura shekara 60

Labarai2023:Gwamna Aminu Tambuwal ya shawarci 'yan Najeriya da kada su sake su zabi dan takarar da ya haura shekara 60
827a29cd89c56849
Duk wanda ya haura shekaru sittin hutu yake bukata ba mukamin siyasa ba

Duk wanda ya haura shekaru sittin a yanzu hutu yake bukata ba mukamin siyasa ba

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya shawarci ‘yan Najeriya da su guji kada kuri’a ga duk dan takarar da ya haura shekaru 60 a zaben shugaban kasa mai gabatowa. Gwamna Tambuwal, mai shekaru 56, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya ba da wannan shawarar ne a jihar Jigawa a ranar Talata, 15 ga watan Maris, bayan kungiyar dalibai ta kasa (NANS) na jihohin arewa 19 sun ‘ amince da’ burinsa, inji rahoton Premium Times.

Kwamishinan matasa da wasannu na jihar Sokoto ya wakilci Gwamna Tambuwal

Gwamnan Wanda ya samu wakilcin kwamishinan matasa da wasanni na jihar Sokoto Bashir Usman a wajen taron.

Jawabin GwamnaTambuwal a wurin taron:

Yan Najeriya Masu jini a jika su suka chanchanta su mulki kasar, duk wanda ya haura shekaru 60 ya kai gargara sai dai fatan gamawa lafiya – amma bai chanchanci neman takara ba.” ya kara da cewa bai kamata ‘yan Nijeriya su daina la’akari da mutanen da ke fama da cututtukan tsufa ba, Gwamnan ya umurci dalibai da su ci gaba da fafutukar ganin an bude cibiyoyin karatun su cikin kankanin lokaci.

Magoya bayan Atiku sun juya masa baya, sun ce yayi tsufa da kujerar shugaban kasa

Kungiyoyin sun zaburo akan bukatar mayar da mulki kudu da kuma bukatar samar da shugaban kasa mai karancin shekaru a 2023 ta bukaci tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dakatar da burin sa ba tsayawa takara, The Guardian ta ruwaito.

Cikin kungiyar akwai manyan shugabannin da ke yi wa Atiku kamfen kamar shugaban kungiyar Turaki Arewa Vanguard na kasa, shugaban kungiyar Middle Belt Network for Atiku; shugaban kungiyar Atiku 2023 ta kudu maso yanma da kuma shugaban kungiyar North4North Support Group for Atiku.
Shugaban kungiyoyin, Femi Osabinu ya bijiro da wannan bukatar ne a wani kwarya-kwaryan taro na manema labarai wanda aka yi a cibiyar kungiyar manema labarai, NUJ da ke Abuja a jiya, inda ya ce Najeriya tana bukatar matashi mai jini a jika don ya samu kuzarin da zai iya tafiyar da mulki.

Kamar yadda yace:

“Duk da Atiku ya yi wa kasa aiki da kyau wanda hakan yasa muke goya masa baya tsawon shekaru, amma maganar gaskiya shekarar sa 77, bai dace ya shiga takara ba. Duk wanda ya kalli halin da kasa take ciki ya kamata ya yi nazari.

“Najeriya tana bukatar matashi mai jini a jika, wanda zai iya jajircewa wurin ganin ya kawo mafita ga kasa da kuma yin ayyukan sa a matsayin sa na shugaba ba tare da gazawa ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe